✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

JIBWIS ta ziyarci Mataimakin Shugaban Kasar Ghana

Shiekh Gombe ya ce Mataimakin Shugaban Ghana ne ya gayyace su kaddamar da sabuwar makarantar koyar da aikin jinya ta Musulunci a Ghana.a.

Shugabannin Kungiyar Jama’atu Izalatul Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS) sun kai ziyara kasar Ghana inda suka gana da Mataimakin Shugaban Kasa, Mahmud Bawumia.

Babban Sakataren JIBWIS, Sheikh Kabiru Haruna Gombe ne ya bayyana hakan cikin wani sako mai dauke da hotuna da ya wallafa shafinsa na Twitter.

Hotunan sun nuna shi tare shugaban Kungiyar Shiekh Abdullahi Bala Lau a gidan Mataimakin Shugaban Ghana.

Shiekh Gombe ya ce Mataimakin Shugaban Ghana ne ya gayyace su domin tattauna batutuwan da suka shafi harakokin addinin Islama.

Ya kuma ce sun halarci wani bikin kaddamar da sabuwar makarantar koyar da aikin jinya ta Musulunci a Ghana.