✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jibrilu daga sama

Wani yaro ne mai suna Jibrilu, aka kai shi makarantar kwana. Gadonsu irin mai bene hawa uku ne, shi kuma yana can na karshe. Cikin…

Wani yaro ne mai suna Jibrilu, aka kai shi makarantar kwana. Gadonsu irin mai bene hawa uku ne, shi kuma yana can na karshe. Cikin dare fitsari ya matse shi, ya rasa yadda zai yi, kawai sai ya fara kuka. Kyaftin ya ji ana kuka, sai ya ce: “Kai, waya ke mana kuka a nan? Sai yaron ya ce: “Jibrilu ne daga sama ta uku!” Haba, nan take dalibai suka yi ta gudu, suna zaton wai mala’ika Jibrilu ne ya shigo dakin.
Daga Usman dangundumar Jama’are, 08093528662