✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Jibi Man United za ta hadu da Chelsea

A jibi Lahadi ce za a fafata a gasar Firimiya ta Ingila a tsakanin kungiyoyin Manchester United da Chelsea. Wasan zai gudana ne a filin wasa…

A jibi Lahadi ce za a fafata a gasar Firimiya ta Ingila a tsakanin kungiyoyin Manchester United da Chelsea.

Wasan zai gudana ne a filin wasa na United, Old Trafford da misalin karfe 4:30 na yamma agogon Najeriya.

Masana harkar kwallo suna ganin wannan shi ne wasan da ya fi zafi a wannan mako a gasar.

Tuni kocin United Ole Gunnar Solksjaer da na Chelsea Frank Lampard suka shirya tsaf don fuskantar wannan wasa don ganin sun samu nasara.

Magoya bayan kungiyoyin biyu suna fata duk kungiyar da ta samu nasara tamkar za ta ba su goron Sallah ne a wasan na jibi.