✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Jibi kuma Super Eagles ta kece raini da Burkina Faso

A jibi Lahadi ne ake sa ran kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles za ta kara a wasa zagaye na biyu da Burkina Faso a…

A jibi Lahadi ne ake sa ran kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles za ta kara a wasa zagaye na biyu da Burkina Faso a filin wasa na Burkina Faso. Wannan wasa ne a kokarin da kasashen biyu ke yi na neman hayewa gasar cin kofin matasa na Afirka da ke wasa a gida da ake kira CHAN Championship da zai gudana a shekara mai zuwa.

A wasan farko da aka yi tsakanin Super Eagles da Burkina Faso a ranar Asabar da ta wuce, Najeriya ce ta lallasa Burkina Faso da ci 2-0 a filin wasa na Adokiye Amesimeika da ke Jihar Ondo. Don haka yanzu kungiyar za ta yi tattaki ne zuwa Burkina Faso don yin wasa zagaye na biyu.
A da an shirya wasan ne a gobe Asabar, amma a ranar Litinin da ta gabata sai Hukumar shirya kwallon kafa ta kasa (NFF) ta bayar da sanarwar ta samu sako daga Hukumar shirya kwallon kafa ta Burkina Faso cewa an canza ranar da wasan zai gudana daga gobe Asabar zuwa jibi Lahadi.
Burkina Faso ta ce ta yi haka ne bayan ta samu amincewa daga Hukumar shirya kwallon kafa ta Afirka (CAF). Ta ce ganin yadda za ta yi wasa zagaye na biyu da Najeriya a kasa da kwanaki bakwai bayan karawar farko ne ya sa ta gabatar da kokenta ga CAF don ta samu sukunin shiryawa wasa na biyu, inda hukumar CAF din ta amince mata da mayar da wasan zuwa jibi Lahadi.
Idan Najeriya ta samu nasara za ta haye rukunin da za ta fafata don hayewa gasar cin kofin Afirka na matasa (CHAN) da zai gudana a shekara mai zuwa.