A karon farko baya shekara shida tsohon Shugaba Kasa Goodluck Jonathan zai hadu da tsohon Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) Farfesa Attahiru Jega, wanda ya jagoranci zaben da Jonathan ya fadi a 2015.
Jonathan da Jega za su hadu ne a Taron Tattaunawar Daily Trust na shekara-shekara, wato Daily Trust Dialogue na 2021 a safiyar Alhamis 21 ga Janairu, 2021.
Daga karfe 10 na safe ne Jonathan zai fara jagorantar taron wanda Jega zai kasance daya daga cikin masu jawabi.
Taken sa na bana shi ne ‘Sauya Tsarin Najeriya: dacewar hakan, yaushe da kuma yadda ya kamata’. Sauya tsarin Najeriya (Restructuring), batu ne da aka jima ana mahawara a kai a kasar.
- Ta yi garkuwa da saurayi saboda ya ki auren ta
- An cafke jami’in tsaron ABU da ke hada baki ana garkuwa da mutane
- Abubuwa 5 da za su sa budurwa ta so ka
Za a nuna taron kai tsaye a gidajen talabijin na AIT da Arise-TV da kuma shafukan sada zumutan Daily Trust wato @daily_trust (a twitter) sai kuma @dailytust (twitter).
Ana kuma a iya halarta daga ko’ina ta adirenshin nan na Webinar: https://zoom.us/webinar/register/WN_b-W7SigrTu-nQq4XY8-QWw
Fitacciyar ’yar jarida, Kadaria Ahmed, ce za ta jagoranci gabatar da taron masana daga bangarorin rayuwa daban-daban daga sassan Najeriya da za su yi jawabi kan batun.
Masu tattaunawa a taron su ne kwararren masanin Kimiyyar Siyasa kuma tsohon Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega.
Sauran masu jawabi su ne dattijo kuma kusa a Kungiyar Al’ummar Yarabawa ta Afenifere, Cif Ayo Adebanjo, sai kuma tsohon Shugaban Kungiyar Kabilar Igbo ta Ohanaeze Nd’Igbo, Cif John Nnia Nwodo.
Daily Trust Dialogue gudunmuwa ce ta kamfanin Media Trust Limited(masu buga jaridar Daily Trust da Aminiya da sauransu), wajen samar wa ’yan Najeriya da ma Afirka fagen tattauna al’amuran kasar da kuma hadin kan Afirka domin samun cigaban siyasa da tattalin arziki a Najeriya da ma nahiyar.
Tun shekarar 2002 Media Trust ke gabatar da taron a duk shekara inda ake tattauna muhimman batutuwan siyasa da shugabanci.
A tsawon lokacin, taron ya samu halarcin shugabannin gwamnatoci, na Majalisar Tarayya da kwararru a fannin kasuwanci, masana’antu da kuma jakadun kasashe.
Za a gudanar da taron ne a dakin taro na NAF Conference Centre and Suites, da ke kan Titin Ahmadu Bello Way, Kado, Abuja, da karfe 10 na safe.
Manyan baki da za su halarci taron sun hada da shugabannin manyan kungiyoyin yankuna da kuma siyasa a Najeriya da suka hada da Majalisar Sarakunan Najeriya (NCTRN), Gammayyar Kungiyoyin Mata ta Najeriya (NCWS), da Majalisar Matasan Najeriya (NYCN).
Akwai kuma Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF), Kungiyar Dattawan Arewa (NEF), Kungiyar Afenifere, Kungiyar Ohanaeze Nd’Igbo da Kungiyar Al’ummar Yankin Arewa ta Tsakiya (NCPF), da sauransu.
Manyan mutane da za su halarci taron sun hada da gwamnoni, ministoci, ‘yan majalisa tsoffi da masu ci.
Akwai kuma shugabannin jam’iyyun siyasa, kungiyoyin kare hakki, kungiyoyin kasashe da kuma jakadun kasashe.
Mukaddashin Shugaban Kamfanin Daily Trust, Nura Mamman Daura, ya fitar ta ce, “sabanin tarukan baya, na bana za a halarta ne a zahiri da kuma ta bidiyo don takaita cudanyar mutane sakamkon annobar COVID-19”.
Mutun 50 da suka hada da Shugaban taron, mai gabatarwa da masu jawabi da wasu manyan baki za su hallara ne a zauren taron, sauran manyan baki da mahalarta kuma za su yi amfani da adireshin webinar da aka bayar don halarta daga duk inda suke ta bidiyo.
Taron na Daily Trust Dialogue gudunmuwa ce ta kamfanin Media Trust Limited domin samar wa ‘yan Najeriya da ma Afirka fagen tattaunawa kan al’amuran da suka shafi kasa, da hadin kan Afirka domin samun cigaba ta fuskar siyasa da tattalin arziki a Najeriya da ma nahiyar Afirka.
Tun shekarar 2002 Media Trust ke gabatar da taron a duk shekara inda ake tattauna muhimman batutuwan siyasa da shugabanci.
A tsawon lokacin, taron ya samu halarcin shugabannin gwamnatoci, na Majalisar Tarayya da kwararru a fannin kasuwanci, masana’antu da kuma jakadun kasashe.
Daily Trust Dialogue ya kuma samu halarcin fitattun mutane da shugabanni daga fadin Afirka.
Daga ciki akwai tsohon Shugaban Kasar Botswana Festus Mogae, tsohon Shugaban Kasar Ghana, Jerry Rawlings, da Dokta Salim Ahmed Salim, Tshohon Fira Ministan Tanzania.
Marigayiya Winnie Mandela tsohuwar matar tsohon Shugaban Afirka ta Kudu, Nelson Mandela; Dr. Mo Ibrahim; da Misis Samia Nkrumah, ‘yar Dokta Kwame Nkrumah na daga cikin wadanda suka taba halartar taron.