Fitaccen jarumin masana’antar Nollywood, John Okafor wanda aka fi sani da Mista Ibu ya riga mu gidan gaskiya.
Mista Ibu wanda ya shahara a matsayin jarumin barkwanci ya mutu yana da shekara 62.
- Amurka ta jefa wa Falasɗinawa tallafin abinci daga jiragen sama
- Magidanta uku na taƙaddama kan mallakar ’ya’yan wata mata a Oyo
Jaridar Business Day ta ruwaito cewa Mista Ibu ya mutu ne a asibitin Evercare da ke Lekki a birnin Ikkon Legas.
Tuni dai magoya baya musamman a dandalan sada zumunta suka shiga alhini, inda suke tunatar da juna irin fina-finan da marigayin ya haska.
Aminiya ta ruwaito cewa a watan Nuwambar bara ne aka yi wa Mista Ibu tiyatar guntule ɗaya daga cikin kafafunsa sanadiyyar ciwon suga da ya addabe shi.
A watan Satumbar bara ne wani bidiyo da Mista Ibu ya wallafa a shafinsa na Instagram ya karaɗe shafukan sada zumunta, inda aka naɗo shi yana neman taimako da kuma addu’a wajen magoya bayansa.
Labarin rasuwarsa na zuwa ne kasa da sa’o’i 24 da rasuwar Quadri Oyebamiji wanda aka fi sani da Sisi Quadri, wani tsohon jarumin Nollywood.