✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jarumin maza

Wani mutum ne za shi masallaci da asuba, yana sanye da babbar riga. Yana cikin tafiya sai ya ji ana neman taimako, ana cewa: “A…

Wani mutum ne za shi masallaci da asuba, yana sanye da babbar riga. Yana cikin tafiya sai ya ji ana neman taimako, ana cewa: “A tare! A tare!!” Sai ya sa babbar rigarsa ya rufe dabbar da ita ya cacume ta. Shi a zaton sa akuya ce aka koro. Mutanen da suka biyo ta sai suka ce masa: “Baba, lallai kai jarumi ne mara tsoro.” Shi kuwa ya ce: “kwarai kuwa, ai na gaji jaruntaka daga babana!” daya daga cikin mutanen sai ya ce wa daya: “Miko mini takunkumin nan in sanya mata.” Da mutumin ya ji haka sai ya ce: “Yaro, me na kama ne?” Ya ce masa: “Kura ce!” Nan take ya tsure da zawo!
Daga Salisu A. Jaji, 07031063622