✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jarumin fim din Hausa Malam Waragis ya rasu

  Allah Ya yi wa jarumin fim din Hausa Malam Muhammad Umar Jos wanda aka fi sani da Malam Waragis ya rasu a garin Jos…

 

Allah Ya yi wa jarumin fim din Hausa Malam Muhammad Umar Jos wanda aka fi sani da Malam Waragis ya rasu a garin Jos da ke Jihar Filato.

 

Al’amin Ciroma ya wallafa a shafinsa na facebook cewa jarumin ya rasu ne bayan ya yi fama da jinya na tsawon lokaci.

 

Tuni aka yi jana’izar mamacin a garin Jos kamar yadda shara’ar musulunci ta tanadar.