✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jarumi Salisu S. Fulani ya angwance

Fitaccen jarumin fim din Hausa na Kannywood Salisu S. Fulani, wanda aka fi sani da Salisun Tsigai ya angwance da amaryarsa Fatima Sa’ad. An daura…

Fitaccen jarumin fim din Hausa na Kannywood Salisu S. Fulani, wanda aka fi sani da Salisun Tsigai ya angwance da amaryarsa Fatima Sa’ad.

An daura aurensa ne a Juma’ar da ta gabata a garin Bolari da ke Jihar Gombe.
Bayan an dauko amarya zuwa Kano ne a ranar Lahadi aka gudanar da wata gagarumar liyafa a dakin taro na Fancy Ebent Hall da ke Kano.
Daga cikin jaruman da suka halarci wannan biki sun hada da Hassan Giggs da Baballe Hayatu da Usman Mu’azu da Sadik Mafia da Isa A. Isa da Ibrahim Sharukhan da Aminu Mai Dawayya da Mas’ud Kanoriders da Yunusa Mu’azu da Naziru danhajiya da Sadik Sani Sadik da sauransu.
Daga bangaren mata kuma akwai irin su Rashida Adamu da Hafsat Shehu da Hadiza Gabon da Samira Ahmed da Hauwa Waraka da Rahama Sirace da Muhibbat Abdulasalam da A’isha Tsamiya da Halima Atete da suaransu.
Baya ga fitowa a fina-finai da ango Salisu S. Fulani ke yi haka kuma shi furdusa ne a wannan masana’anta ta Kannywood a karkashin kamfaninsa mai suna S. Fulani Productions. Daga cikin fina-finan da ya yi sun hada da Lubuna da Munubiya.
Mutane da yawa na tunanin cewa Salisu S. Fulani kani ne ga marigayiya Hussaina Tsigai, sai dai ba haka ba ne. Aminiya ta kalato cewa kasancewar garinsu daya da marigayiya Tsigai wato Jihar Gombe, shi ya sa lokacin da ya tashi shiga farkar fim ya shigo ta hannunta.