✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jaruman Bollywood 5 da suka sadaukar da dukiyarsu ga mutane

A cikin kowace al’umma akan samu mutanen da suke sadaukar da wani abu daga dukiyarsu ga marasa galihu ko masu dauke da wata lalura da sauransu.…

A cikin kowace al’umma akan samu mutanen da suke sadaukar da wani abu daga dukiyarsu ga marasa galihu ko masu dauke da wata lalura da sauransu.

A bangaren jaruman masana’antar fina-finai ta Indiya (Bollywood) ma, akwai irin wadannan mutane, wadanda ba sa damuwa da abin da suke samu wajen sadaukar da shi ga mabukata.

Wadansu daga cikin irin wadannan jarumai ma suna da kungiyoyin agaji na kashin kansu baya ga taimakon da suke yi a gefe guda.

Ga biyar daga cikin jaruman Bollywood da ke sadaukar da dukiyarsu ga mabukata kamar yadda gidan rediyon BBC ya tattara.

 

Shah Rukh Khan

Shah Rukh Khan na daga cikin jaruman Bollywood da suke taimaka wa marasa galihu ko masu wata lalura.

Kudin da wani ayarinsa ya samu a wata gasa da aka yi bayan lashe gasar da suka kai  Crore 15 na kudin kasar Indiya, kwatankwacin Dalar Amurka miliyan 195 da dubu 983 da 700, ya sadaukar ga masu fama da lalurar cutar daji wato kansa da ke zaune a Mumbai da Kolkata.

 

Shilpa Shetty

Jarumar da ta ja hankalin jama’a lokacin da ta ci gasar Big Brother ta Birtaniya da aka yi a shekarar 2007.

Ta samu Fam dubu 100 wadda ta yi kusan crore 1, ga kungiyoyin da ke wayar da kai ga masu cutar kanjamau da ke karya garkuwar jiki.

 

Salman Khan

Salman Khan, dama tuni ya yi alkawarin cewa duk kudin da zai samu daga fim, to kashi 10 cikin 100 na kudin ne kawai zai dauka ya yi amfani da su don kashin kansa, amma sauran kashi 90 cikin 100, zai rika bayarwa ne ga mabukata ko masu dauke da wata lalura da suke neman taimako.

Ba sau daya ba sau biyu ba, Salman Khan ya sha taimaka wa wadansu daga cikin abokan aikinsa da suka shiga wata damuwa ta rashin kudi ko suke fama da wata lalura.

 

Nana Patekar

Jarumin wanda har yanzu ke zaune a gidan da bai taka kara ya karya ba tare da iyalansa, yana sadaukar da kashi 90 cikin 100 na kudin da yake samu a fim ga mabukata.

Duk da irin fitattun fina-finan da Nana Patekar ke yi, kudi ba sa gabansa, sai dai taimako ga marasa karfi.

Yana rayuwa daidai misali domin babu abin da ya rasa, amma bai tara wata dukiya ta a-zo-a-gani ba, saboda duk ya sadaukar da ita.

 

Sonam Kapoor

Matashiyar jarumar tana bayar da kyautar abubuwan da ta mallaka, ba kudi ba kawai hatta kayanta na sawa.

Akwai lokacin da Sonam ta kwashe kayanta na sawa gaba daya ta kai gidan marayu domin a raba wa wadanda za su iya sanyawa.

Abin hannunta bai rufe mata ido ba, haka kudinta na fim ma idan ta yi, takan kwashi kaso mai girma ta bai wa mabukata ko masu lalurar rashin lafiya domin su yi magani.