Mutum tara, ciki har da wani jariri, sun riga mu gidan gaskiya bayan wata mota da ta kwace ta shiga har cikin gida ta kade su a kasar Filifins.
’Yan sanda a Arewacin kasar ta Filifins sun tabbatar cewa motar ta kwace ne a daidai wani kwana, ta auka wa wasu jerin gidaje da ke gefen wani babban titi a garin Lal-Lo da ke lardin Cagayan.
- AFCON2021: A karon farko, Senegal ta daga Kofin Afirka
- Kungiyar Tarayyar Afirka ta zabi sabon shugaba
Mutanen da suka rasu, “Suna shan iska ne a gaban gidan wani abokin arzikinsu lokacin da motar da ta kwace ta fado a kansu,” a cewar Jefferson Mukay, babban jami’in dan sanda na garin Lal-Lo.
Da yake bayani a safiyar Litinin, Mukay ya bayyana cewa motar ta kwace wa matukinta ne a ranar Asabar da dare a sakamakon gudun wuce kima da yake shararawa.
Ya kara da cewa an kai direban motar da abokinsa da ke cikin motar asibiti a cikin halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai.
Mukay ya kuma shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa za a gurfanar da direban a gaban kotu kan zargin aikata kisa fiye da sau daya.
AFP ya ruwaito cewa ana yawan samun hatsarin mota a kasar ta Filifins, inda direbobi ke yawan saba dokokin tuki, gami da daukar kaya fiye da kima da kuma rashin kula da lafiyar motoci yadda ya kamata.
A cikin watan Janairun da ya gabata, wasu mutum 11 da ke kan hanyarsu ta zuwa casu sun rasu bayan motarsu ta kwace ta yi adungure da su a yankin Kudancin kasar.