Shugaba Muhammadu Buhari ya yi alhinin mutuwar tsohon Babban Hafsan Hafsoshin Tsaro, Laftanar Janar Joshua Dogonyaro (mai ritaya).
Shugaban kasar ya bayyana takaicinsa ne cikin wani sako da Kakakinsa, Mallam Garba Shehu ya fitar ranar Alhamis a Abuja.
Ya bayyana mutuwar Dogonyaro a matsayin “babban rashi ba kawai ga sojojin Najeriya ba, har ma ga kasar saboda sadaukar da kai da kishin kasa wajen kare martaba da hadin kanta.”
Ya ce, “Mutuwar Dogonyaro ta yi matukar girgiza ni domin a matsayina na soja, na san radadin da aka ji idan aka rasa irin wannan jami’i wanda ya yi iyaka bakin kokarinsa wajen hidimtawa kasar nan,” in ji shi.
Shugaban ya kuma bayyana Dogonyaro a matsayin hazikin jami’i wanda ya kware a fagen aikin soja.
Buhari ya kuma mika sakon ta’aziyyarsa zuwa ga Gwamnati da al’ummar Jihar Filato dangane da mutuwar “wannan fitattacen Janar din soji.”
Tarihi ya tabbatar da cewa, a ranar 27 ga watan Agustan shekarar 1985 ce sojoji karkashin jagorancin Janar Ibrahim Badamasi Babangida suka hambarar da Gwamnatin Janar Muhammadu Buhari a wani juyin mulki da ba a zubar da jini ba.
Marigayi Dogonyaro wanda ya mutu ranar Alhamis a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos da ke Filato, shi ne ya gabatar da jawabi a madadin sojojin da suka kitsa juyin mulkin da aka yi wa Gwamnatin Buhari.
Yayin jawabin shekaru 36 da suka gabata, Dogonyaro ya zargi Buhari da yin fatali da muradin al’ummar Najeriya a wancan lokaci.
Kazalika, ya yi ikirarin cewa Gwamnatin Buhari ta dora alhakin gazawarta a kan gwamnatin farar hula ta Shehu Shagari.