✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jamus ta kara wa Ukraine makamai masu linzami 2,700

Makamai masu linzami sama da 2,000 Jamus ta ba wa Ukraine a cikin kwana biyu domin kakkabo jiragen Rasha

Gwamnatin Jamus ta yi wa Ukraine alkawarin karin makamai masu linzami guda 2,700 domin kakkabo jiragen sama, kan mamayar da Rasha ta yi wa kasar.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito wani jami’in gwamnatin Jamus na cewa gwamnatin kasarsa ta “amince da ba wa Ukraine karin taimako’, ta hanyar tura mata makamai masu linzami samfurin STRELA domin kakkabo jirage.

A kwana biyun da suka gabata Jamus ta ba wa Ukraine makamai masu linzami sama da 2,000 domin kakkabo jirage saboda mamayar Rasha a kasar.

Hakan na zuwa ne a yayin da gwamnatin ta Jamus ta sanar da shirinta na kashe wa rundunar tsaronta Dala biliyan 100 domin fuskantar duk wata barazana daga kasar Rasha.

A ranar Laraba, a karon farko Jamus ta aike wa Ukraine da wasu makaman tarwatsa tankokin yaki guda 1,000 da makamai masu linzami na kakkabo jiragen sama guda 500.

Matakin tura makaman da Jamus ta dauka a wannan karo ya biyo bayan sauya matsayin da ta yi ne daga tsarinta na kin tura makamai zuwa wuraren da ke fama da rikici.