✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jam’iyyu 45 sun marawa dan takarar Gwamnan APC a Gombe baya

Jam’iyyun adawa 45 a jihar Gombe karkashin gamayyar hadakar jam’iyyu ta IPAC sun amince da marawa dan takarar Gwamnan jihar Gombe a jam’iyyar APC Alhaji…

Jam’iyyun adawa 45 a jihar Gombe karkashin gamayyar hadakar jam’iyyu ta IPAC sun amince da marawa dan takarar Gwamnan jihar Gombe a jam’iyyar APC Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya baya a zaben da za a yi ranar Asabar.

A wata sanarwa da shugaban IPAC ya fitar na cewa, sun yanke shawarar marawa dan takarar Gwamnan APC baya ne bayan ganawar da suka yi da sauran jam’iyyun adawa.

Wasu daga cikin jam’iyyun da suka marawa Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya baya sun hada da: Accord Party, DPP, ADC ACD, AD, MPN, CAP, BNPP, APA, AA, MMN, ANP, PPC, HDP, UPN, NCP, UPP, NCMP da PAC da dai sauransu.