“Na ce mu karanta Kundin Tsarin Mulkin Kasar nan, domin ba zan yi kuskuren yunkurin in nemi wa’adin mulki karo na uku ba, ko makamancin wani abu mai kama da haka. Bayan shekaru da suke cin mini. Na yi rantsuwa da Alkur’ani Mai girma da na yi imani da shi, cewa zan bi tanade-tanaden da Kundin Tsarin Mulkin Kasar nan ya tanada, da ya ce zango biyu kawai zan yi.”
“Na san yanzu ina cikin zango na biyu kuma na karshe, zan iya kasancewa sai yadda na yi, kasancewar ba wanda zan kara neman ya ba ni kuri’arsa.”
Wadannan wasu ne daga cikin kalaman Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi ke nan a wajen taron Kwamitin Zartarwar Jam’iyyar APC ta Kasa da aka gudanar a Abuja Babban Birnin Tarayya a ranar Juma’a 29 ga Nuwamban da ya gabata.
Shugaba Buhari ya nanata niyyarsa ta tabbatar da ganin jam’iyyarsu ta APC ta ci gaba da rike kambinta na mulkin kasar nan, koda ya bar mulki a shekarar 2023, in Allah Ya kai mu. Amma ya tunatar da ’ya’yan jam’iyyar cewa nasarar jam’iyyar ba za ta dore ba, har sai kowane zababbe ya ci gaba da kasancewa mai kima da martaba a idons mutanen mazabarsa, don haka sai ya shawarci irin wadannan zababbu su ci gaba da kasancewa masu mutunci a mazabunsu.
Shugaba Buhari ya sake tunatar da ’ya’yan jam’iyyar cewa tarihi ba zai taba yafe musu ba, idan har jam’iyyarsu ta APC ta wargaje bayan wa’adin mulkinsa.
Yana mai cewa “Idan har a kan wani dalili kuka raba jam’iyyar, ko daga mazaba ce, wanda zai janyo faduwarta, to, ku zama cikin shirin tarihi ba za a taba tunawa da ku ba a zaman shugabanni nagari har abada.”
Karon farko da Shugaba Buhari ya fara furucin ba zai nemi TAZARCE ba, shi ne lokacin da yake cikin rangadin jihohin kasar nan a lokacin gangamin neman kuri’a a zaben bana, sai kuma a wannan karo.
Sashe na 137, karamin sashe na 1(b), na Kundin Tsarin Mulkin Kasar nan shi ya yi tanadin hanin TAZARCE.
Idan wancan bayani na farko Shugaba Buhari ya yi shi ne don neman masu kada kuri’a su sake kada masa. Jawabinsa na baya-bayan nan bai rasa nasaba da irin kiraye-kirayen da wadansu ’ya’yan jam’iyyarsa ta APC suka fara tun bayan da a watan jiya Kotun Koli ta tabbatar masa da nasarar lashe zaben bana, bayan sauraren daukaka karar da dan takarar Jam’iyyar PDP kuma tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Alhaji Atiku Abubakar da ita kanta jam’iyyarsa ta PDP suka daukaka.
A duk cikin masu wadannan kiraye-kirayen Buhari ya yi TAZARCE, ba wanda ya fi nuna da gaske yake irin Mista Charles Enya wani dan Jam’iyyar APC da ya shigar da wata kara a Babbar Kotun Tarayya yana neman kotun da ta tilasta wa Majalisar Dokoki ta Kasa a kan sai su gyara duk wani sashe na Kundin Tsarin Mulkin Kasar nan da ya yi tanadin hana yin TAZARCE, wato neman zango na uku ga Shugaba Buhari, bayan ya kammala wa’adinsa na biyu a shekarar 2023, in Allah Ya kai rai.
Zuwa yanzu rahotanni sun tabbatar a ranar Larabar makon jiya, Mista Charles bisa ra’ayin kansa ya koma kotun inda ya janye karar.
Tun ma kafin janye waccan kara da kiraye-kirayen Buhari ya yi TAZARCE, ita kanta Jam’iyyar APC da Majalisar Dattawa da jam’iyyun adawa sun yi ta tir da Allah wadai ga irinsu Mista Charles, da ma kokarin daukar mataki, walau na ladabtarwa ko na kafa doka da za ta magance niyyar masu irin wadancan kiraye-kirayen yin TAZARCEN.
Alal misali, an ruwaito Kakakin Jam’iyyar APC ta Kasa Lanre Issa Onilu, yana fada wa manema labarai a Abuja cewa masu kiraye-kirayen TAZARCEN, ba suna yi ba ne a bisa doka, har ma ya bayyana wadancan mutane da makiya mulkin dimokuradiyya da neman yi wa mulkin zagon kasa.
Lanre ya yi alwashin muddin Jam’iyyar APC ta bincika ta kuma tabbatar da cewa Mista Charles dan jam’iyyar ce, to ba makawa za ta kore shi daga jam’iyyar.
A gefe daya ita ma Majalisar Dattawa ta dukufa wajen ganin ta zartar da wani daftarin doka da zai tanadi hukuncin dauri ko tara ko duka biyu ga duk wani dan kasar nan da ya yi kokarin kawo tarnaki a shirye-shiryen mika mulki daga wata gwamnati zuwa wata a kasar nan.
Batun Shugaba ya zarce a mulkin kasar nan, batu ne mai dadadden tarihi, kusan yau shekara sama da 40. Koda yake Janar Yakuba Gowon da ya mulki kasar nan tsawon shekara 8 daga 1967 zuwa 1975, a zamansa na Shugaban mulki soja bai taba nuna kwadayin zai nemi TAZARCE ba, illa jan kafar da ya rika yi na kasa fito da jadawalin ranar da zai mika mulki a hannun farar hula. Hakan ya janyo a 1975, sojoji suka yi masa juyin mulki inda marigayi Janar Murtala Ramat Mohammed ya hau mulki a 1975.
Tsohon Shugaban mulkin soja Janar Olusegun Obasanjo da ya gaji Janar Murtala ya zauna a kan jadawalin da gwamnatinsu ta tsara na mika mulki a hannun farar hula, don haka bayan juyin mulkin da aka kashe Janar Murtala a ranar 13 ga Fabrairun 1976, Janar Obasanjo ya tabbatar da mika mulki a hannun zababbiyar gwamnatin farar hula ta Alhaji Shehu Shagari na Jam’iyyar NPN a ranar 1 ga watan Oktoban 1979.
Batun yin TAZARCE ga gwamnatin farar hula ta Shugaba Shagari, bai ma taso ba, kasancewar yana da wata uku a zangonsa na biyu a ranar 31-12-1983, sojoji suka yi masa juyin mulki, suka dora Shugaba Janar Muhammadu Buhari. Shi ma Shugaba Janar Buhari wata 20 ya samu a karagar mulki, daga Janairun 1984 zuwa Agustan 1985, don haka bai samu mike kafa ba a mulki bare a yi masa tayin yin TAZARCE, sai Janar Ibrahim Badamasi Babangiga ya hau.
Janar Babangida da ya shafe shekara takwas cur (1985 zuwa 1993) bayan ya gaji Janar Buhari da Janar Sani Abacha da ya hambarar da gwmnatin rikon kwarya ta wata uku kacal Agusta zuwa Nuwamban 1993, ta Cif Ernest Shonekan da shugaba Obasanjo a zaman Shugaban gwmnatin farar hula shekara takwas 1999 zuwa 2007, su ne shugabanni uku na kasar nan da suka fitar da maitarsu a fili a kan ko ana ha-maza ha-mata sai sun yi TAZARCE. ’Yan kasa da ma na duniya sun ga irin yadda Allah Ya kawar da su daga kan karagar mulki a lokacin da ba su shirya barin mulkin ba.
Da wannan dan tarihi nake ganin bai kamata yanzu ko nan gaba wani Shugaba ya kwadaita wa kansa zuga da kiraye-kirayen mabiya a kan ya yi TAZARCE ba, don zuwa yanzu duk dan kasa ba ma masu mulki ba, sun ga yadda Allah Yake kunyata shugabannin da suka nemi yin TAZARCE a kan karagar mulkin kasar nan.
Da fata Shugaba Buhari da jam’iyyarsa ta APC za su dauki darasi.