✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jam’iyyar APC ta lashe zaben kananan hukumomin Jihar Sakkwato

Jam’iyar APC ta lashe zaben shugabannin kananan hukumomi 22 da kansiloli 234 na Jihar Sakkwato da gudanar a ranar Asabar da ta gabata.Shugaban Hukumar Zabe…

Jam’iyar APC ta lashe zaben shugabannin kananan hukumomi 22 da kansiloli 234 na Jihar Sakkwato da gudanar a ranar Asabar da ta gabata.
Shugaban Hukumar Zabe ta Jihar, Alhaji Usman Abubakar ne ya sanar da hakan a taron manema labarai da ya kira a hedikwatar hukumar da ke Unguwar Mabera a birnin Sakkwato.
Shugaban ya ce ba su yi zabe a karamar Hukumar Gudu ba, saboda rashin sunan Jam’iyyar PDP a takardun jefa kuri’a wanda hakan ya sanya suka dage zaben zuwa wani lokaci.
 Shugaban ya gode wa jama’ar jihar kan halin dattaku da suka nuna wajen gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da lumana a duk fadin jihar da kuma hadin kan da suka bayar wajen aiki da na’urar tantance masu kada kuri’a domin kara inganta zaben.
Mai shari’a Afolabi Abdulfatah Adeyinkan Shugaban Hukumar Zabe ta Jihar Legas a ziyarar ganin yadda aka gudanar da  zaben ya jinjina wa Hukumar Zabe ta Jihar Sakkwato kan amfani da katin dindindin na zabe da kuma na’urar tantancewa da aka yi zaben da su.
Ya nuna farin ciki kan yadda zaben ya gudana, inda ya ce duk wanda ya samu nasara to shi ne jama’arsa suka zaba domin an yi maganin duk wani magudi a lokacin gudanar da zaben, kuma ya jinji wa gwamnatin jihar kan wannan nasara da hukumar zabe ta jihar ta samu.
A bangaren Jam’iyyar PDP kuwa Sakatarenta Alhaji Kabiru Aliyu ya shaida wa Aminiya cewa “Wannan ba zabe aka yi ba, nadi ne da yaudara, domin tun kafin a kammala zaben aka shirya wadanda suka yi nasara kuma suka fade su. Ka ga ba a yi zabe a karamar Hukumar Gudu ba, wannan ya faru ne domin sun tabbatar ba wata hanyar yin magudi a can kamar sauran kananan hukumomi da suka yi kama-karya. Jam’iyyarmu na shirin daukar matakin da ya dace kan zaben da aka kira wai an yi, amma dai duk wani dan jihar nan yana da yakinin ba a yi zaben gaskiya da adalci ba. Kuma muna kira ga jama’armu su kwantar da hankalisu za mu kwato musu hakkin ta hanyar da ta dace kuma mun jinjina musu kan kokari da jajircewar da suka yi na son Jihar Sakkwato ta samu ci gaba, amma duniya ta sani mun yi fatali da sakamakon wannan zaben da aka rika satar akwati da dangwala wa dan takara tun kafin shiga filin zabe.”