Idan muka yi la’akari da abubuwan da ke gudana, alama ta nuna cewa APC na hankoron maye gurbin PDP ne kawai amma ba domin ta kawo canji ba, ko kuma domin ta dara ta nuna kyautatawa ba. Abin da Najeriya ke bukata, ba wai kawai a samu kawar da wasu mulaka’u a maye gurbinsu da wasu shigensu, masu son dadada wa kansu ba. Abin da ake bukata shi ne, a samu wadanda za su daga martabar Najeriya da al’ummarta daga zaluncin mulaka’u.
Muna bukatar tsarin siyasa mai inganci, wanda zai kawar da zalunci, ya karfafa da bunkasa Najeriya ta hanyar amfani da albarkatun da Allah Ya hore mata wajen bunkasa al’umma da kyautata masu. Muna bukatar tsarin siyasar da zai tabbatar da doka da oda, ta yadda doka za ta zama mai karfi, wadda za ta iya taka duk wanda ya taka ta, ba tare da la’akari da iko ko mukaminsa ba.
Sai dai abin ba haka yake ba a yanzu, domin kuwa tsarin ya doru ne bisa zalunci, yadda shugabanni suka kware wajen muguwar sata, almundahana, cin hanci da rashawa da sauransu. Shekaru 15 da suka gabata, PDP ta share wa azzaluman ’ya’yanta hanya, yadda ta mayar da dukiyar Najeriya ‘daga-ita-sai-’ya’yanta.’ Wannan dalili ne ya sanya mutane irin su Obasanjo da Babangida da Tony Aninih da Pius Anyim a kullum suke kara azurcewa alhali sauran ’yan Najeriya na kara talaucewa.
Don haka, babban kalubalen da ke gaban ’yan kishin kasa, ba wai kawai su kawar da azzaluman shugabanni ba ne, a’a, kalubalen shi ne, su kawo sauyi a siyasa, ta yadda tsarin zai inganta, yadda za a hana satar dukiyar al’umma, yadda zai zama abin wahala a ce wata jam’iyya ta zo da tsarin da zai kassara Najeriya, tsarin da kawai zai amfani ’ya’yanta ita kadai.
Babbar tambayar da ke zuciyata ita ce, shin ko APC tana da karfin kishin kasa da karsashin kawo ingantaccen sauyi nakawarai ga kasar nan?
A can baya, kamar yadda na fada, an cusa Najeriya cikin bahallatsen tsarin siyasa, wanda ya kyankyashe muggan shugabanni, masu danne talakawa da sace masu dukiya. Shugabannin da suka kware wajen halaka al’umma, ba raya su ba. Tsarin da ya haifar da yanayi mai ban takaici da ban kunya, inda kasa da mutum 300 suka babbake da wawashe dukiyar kasa su kadai, wanda haka ya hana ta samun mutunci a idon duniya.
APC, idan har da gaske take yi, to ya kamata ta yi watsi da tatsuniyar da muke ta ji, cewa kawai tana son kawar da PDP ne ba matsalolinta ba. Ya kamata tun yanzu ta nuna cewa a shirye take, za ta iya bayar da ingantaccen shugabanci, za ta iya kyankyashe zakakuran shugabanni masu kishin kasa da ’ya’yanta.
Ga wasu abubuwa nan, abin lura da tambaya: Wane ne zai iya kawo bayani gane da bin doka da oda? Wane ne zai ba mu tabbacin cewa wannan jam’iyya ta zo ne domin ta bauta wa al’umma, ba domin ta bauta wa kanta da ’ya’yanta kadai ba?
A nan, ba ina nufin, a zo da batutuwa rararara ba, wato a rika fadi da baki kawai ba. A’a, ta yaya za a aiwatar da kudurori da alkawuran a aikace? Na san cewa lallai APC tana da ’ya’ya masu karfin azancin kalami, sai dai a nan ba magana kawai muke so ba, sai aiki. Ya dace a samu wannan tun daga yanzu, a samu tsari da manufofi masu nagarta, wadanda suka dace da tsarin mulkin kasarmu, sannan kuma mu gani a kasa, tun kafin ma a ce za a zo ga zaben 2015.
Idan aka samu haka a APC, lallai zai zama babban kalubale ga sauran jam’iyyu, sannan kuma al’umma za su ce lallai sauyi ya zo; kamar kuma yadda za su amince da cewa a yanzu kam APC da gaske take wajen yi wa al’umma hidima.
Idan ba haka ba kuwa, to kaicon APC idan ba ta bambanta kanta da PDP ba, musamman idan ta bi Yarima domin ta sha kida. Idan ba ta bambanta da PDP ba ta wajen tsari da aiki mai kyau ga al’umma, ta zama daidai da ita. To shi ke nan, abin ya zama abin kunya da takaici. Kuma lallai abu ne mai hadarin gaske ga kanta, ga kasa a ce ta zama kamar PDP.
Ga wasu shawarwari da zan ba APC, domin ta cimma kudurinta na kawo canji: Ya kamata gwamnonin APC su canja tako tun yanzu, su nuna cewa talakawa suke wa aiki, maimakon da suke nuna cewa su mulaka’u ne. Ya dace jam’iyyar ta tsaro da wani shiri na ladabtar da gwamnanta tun kafin ya sauka, idan ya ci amanar talakawa. Ya kamata APC ta ba dokar nan da ake son kafawa goyon baya, wacce za ta haramta wa gwamna tsayawa takarar zama dan Majalisar Tarayya, har sai bayan shudewar zabuka biyu bayan saukarsa. Ya dace jam’iyyar ta sara yadda za ta mutunta dokokin zabe. Haka kuma, jam’iyyar ya kamata ta wallafa dukan hanyoyin da za ta bi wajen yaki da satar dukiyar al’umma da cin hanci da rashawa, a sanar da al’umma. Ya dace kuma jam’iyyar ta shirya gangamin wayar da kan al’umma game da katin zabe da sauransu a fadin kasar nan.
APC dai ya dace ta gane cewa, ba wai kawai muna bukatar ta canja PDP ba ne, a’a sai ta kawo canji mai ma’ana ga al’umma wanda ya dace da ci gaba.
Jam’iyyar APC ko PDP: Wace ce ba wace ce ba? (2)
Idan muka yi la’akari da abubuwan da ke gudana, alama ta nuna cewa APC na hankoron maye gurbin PDP ne kawai amma ba domin ta…