✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jam’iyyar Al-Mustapha ta janye kararta kan zaben Tinubu

Jam'iyyar AA ta janye karar da ta shigar na kalubalantar nasarar Bola Tinubu na jam'iyyar APC a zaben shugaban kasa na 2023.

Jam’iyyar AA ta janye karar da ta shigar na kalubalantar nasarar Bola Tinubu na jam’iyyar APC a zaben shugaban kasa na 2023.

Jam’iyyar, wadda dan takararta na shugaban kasa shi ne Hamza Al-Mustapha, tsohon dogarin tsohon shugaban kasa na mulkin soji, Janar Sani Abacha, ta janye karar ne a ranar Litinin.

Lauyan Jam’iyyar, Oba Maduabuchi, ne ya sanar da haka a yayin da kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta fara zama. Sai dai kuma bai bayyana dalili ba.

Bayan wadanda ake kara, wato jam’iyyar APC da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) sun ce ba su da ja game da matakin, sai Alkali Haruna Tsammani ya soke karar ta AA.