✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jami’iyya ta kori dan takararta kan yabon Hitler a Italiya

Jam’iyar dai ta dade a kasar tun zamanin tana matsayin kungiyar mulkin kama-karya da aka kafa bayan Yakin Duniya na Biyu.

Jam’iyyar Brothers Party da ake hasashen za ta lashe zabuka a kasar Italiya, ta dakatar da wani dan takararta a ranar Talata, bayan ya yabi mulkin tsohon jagoran kama-karya, Adolf Hitler ta yanar gizo.

Jam’iyar dai ta dade a kasar tun zamanin tana matsayin kungiyar mulkin kama-karya da aka kafa bayan Yakin Duniya na Biyu.

To sai dai jagorarta ta yanzu, Giorgia Meloni, da ake sa ran za ta zamo Fira Ministar kasar ta gaba, ta nesanta jam’iyyar da wannan akida.

To sai dai masu sharhi kan lamuran yau da kullum na kasar na ganin har yanzu akwai burbushin masu akidar kama-karya rike da madafun ikio da dama a kasar.

Jaridar La Repubblica a kasar ta wallafa wani rubutu a shafin sada zumunta wanda dan takarar jamiyar, Calogero Pisano, ya yi shekaru takwas da suka gabata, yana yabon Hitler.

Ko a baya ma, Pisano wanda ke takara a tsibvirin Sicily, ya taba yabon wani da ya alakanta wani fitaccen dan siyasa da riko da akidar ta kama-karya ta zamani a shekarar 2016.

Sai dai fitowar wannan rubutun nasa na yanzu, ya janyo masa fushin Yahudawan kasar.

Wata shugabar al’ummar Yahudawa a birnin Roma, Ruth Dureghello, ta mayar masa da martani ta shafin Twitter, tana cewa “A ce wadanda ke yabon Hitler za su iya zamowa ’yan majalisa abin Allah wadai ne.”

A nasu bangaren ’ya’yan jam’iyar Brothers sun ce tuni sun dakatar da Pisano, tare da fitar da sanarwar nesanta jam’iyar da shi.

Shi ma dai Pisano ya ce yana nadamar rubuce-rubucen da ya yi a baya, domin har ya goge su, tare da neman afuwar al’umma.