✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jami’ar Gombe ta daga likafar malamai 10 zuwa matsayin Farfesa

An bai wa wasu 13 masu digirin digirgir mukamin daf da Farfesa wato Readers.

Jami’ar Jihar Gombe ta daga likafar malamai 10 zuwa matsayin Farfesa tare da bai wa wasu 13 masu digirin digirgir mukamin daf da Farfesa wato Reader.

Jami’ar ta daga darajar malaman ne a yayin zaman Majalisar Gudanarwar Jami’ar karo na 48 da ta gudanar a makon nan.

Wannan batu yana kunshe ne a wata takarda mai dauke da sa hannun Magatakardar Jami’ar, Dokta Abubakar Aliyu Bafeto, a madadin Shugaban Jami’ar, Farfesa Usman Aliyu El-Nafaty, wanda kuma shi ne Sakataren Kwamitin Gudanarwar Jami’ar.

A cewarsa, malaman da suka samu karin girman an zakulo su ne daga bangarorin ilimi daban-daban na jami’ar kama daga bangaren nazarin Likitanci Kananan Yara (paediatrics), da sashin Hade-Haden Magunguna (Chemical Pathology) da sashin nazarin Tsirai (Botany) da kuma bangaren daukar hoton jikin dan Adam wato Radiology da sauran su.

Malaman da suka samu karin girman zuwa matsayin Farfesa sun hada da Dokta Iliya Jalo, Dokta Sani Adamu da Dokta Danladi B Adamu da Dokta Halima M Abba da Dokta Hankouraou Seydou

Sauran sun hada da Dokta Danladi M Umar da Dokta Kennedy D Yoriyo da Dokta Bulus Wayas, da Dokta Lazarus Abore Mbaya da kuma Dokta Mohammad M Manga.