Mataimakin Shugaban Jami’ar Bayero da ke Kano mai kula da al’amuran Gudanarwa, Farfesa Haruna Wakili ya riga mu gidan gaskiya.
Farfesa Wakili wanda shehin malami ne a Sashen Nazarin Tarihi na jami’ar, ya rasu da sanyin safiyar Asabar a Asibitin Kasa da ke Babban Birnin Tarayya Abuja bayan wata gajeriyar jinya.
Kafin rasuwarsa, Farfesan ya taba rike mukamin Kwamishinan Ilimi a Jihar Jigawa, ya kuma taba zama Darakta a Cibiyar Bincike da Bayar da Horo kan Harkokin Dimokradiyya ta Malam Aminu Kano (Mumbayya House) da ke Kanon.
Da yake tabbatar da rasuwar, tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, wanda Farfesan ya yi kwamishina a lokacin mulkinsa ta bakin kakakinsa, Mansur Ahmed ya bayyana rasuwar Farfesa Haruna Wakili a matsayin babban rashi, tare da addu’ar Allah Ya kyautata makwancinsa.
- Fitattun mutum 10 da suka rasu cikin mako daya a mace-macen Kano
- Mace-macen Kano: Sakamakon bincike sun yi karo da juna
- Coronavirus: Matashi ya kirkiri na’urar wanke hannu a Kano
It ma da take tabbatar da rasuwar, Rijitarar Jami’ar ta Bayero, Fatima Binta Mohammed ta nuna kaduwarta, tana mai cewa mutuwarsa babban rashi ce ga jami’ar.
Ta ce nan ba da jimawa ba za a gudanar da jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.