✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jami’ar Bayero ta fara Diflomar Gaba da digiri a fannin Karatu

Za a rika yin kwas din da hadin gwiwar Jami'ar Florida ta kasar Amurka.

Jami’ar Bayero ta Kano (BUK) ta fara karatun Difloma na gaba da digirin farko a fannin Koyon Karatu don farfado da dabi’ar karatu da ingantaccen koyo a kowane mataki.

Cibiyar Bincike da Cigaban Karatu ta Najeriya (NCRRD) wadda ke Jami’ar tare da hadin gwiwar Sashen Turanci na Jami’ar ne suka kaddamar da fara kwas din tare da tallafin Jami’ar Florida ta Amurka.

Daraktar cibiyar,  Farfesa Talatu Musa Garba ce ta bayyana haka a wurin bude taron kasa na shekara-shekara karo na uku kan Koyar da Karatu a Matakin Farko a Najeriya.

Ta ce an samar da cibiyar ne domin hada kan masu ruwa da tsaki domin bunkasa sha’anin koyon  karatu a matakin farko a Najeriya.

“Cibiyar za ta mayar da hankali ne wajen bayar da darussa daban-daban tare da hadin gwiwar Sashen Ilimi na Jami’ar  Bayero da hadin gwiwar Jami’ar Florida,”  inji daraktar.

Yanzu an kammala shiryen-shiryen tabbatar da fara Diflomar gaba da digirin farko a fannin Koyon  Karatu wanda aka fara talla ga masu sha’awa a shafin jami’ar.

“Haka kuma an kammala shirye-shiryen fara gudanar da karatun a matakin shaidar satifiket a kan Koyarwar da Karatun a Matakin Farko a watan Yuli 2022,” inji ta.

A nasa jawabin, Shugaban Jami’ar  BUK, Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya ce yarjejeniyar da aka kulla tsakanin jami’o’in ce ta kai ga kafa cibiyar a makarantar.

Ya ce yarjejeniyar ta ba wa malaman jami’ar damar samun horo mai zurfi a kan bincike da Koyar da Karatu a Jami’ar Jihar Florida har na tsawon wata shida.

Ya kara da cewa a yanzu haka an kammala kashi 95 cikin 100 na ginin cibiyar a jamiar tare da  samar da kayan aikin da suka kamata.