Jami’ar Bayero ta Kano ta ayyana Litinin, 24 ga watan Oktoban 2022 a matsayin ranar komawar dalibai domin ci gaba da karatu.
Wannan dai na zuwa ne yayin da tuni malaman jami’ar suka koma bakin aiki a yau Litinin bayan Kungiyar Malaman Jami’o’in kasar ta sanar da janye yajin aikin da suka shafe wata takwas suna yi.
Cikin wata sanarwa da Matamakin Magatakardar Jami’ar, Lamara Garba ya fitar, ya ce ayyana ranar komawar ta biyo amincewar da Majalisar Gudanarwar Jami’ar ta yi bayan wani zama da ta gudanar a ranar Alhamis ta makon jiya.
Dalibai da ma’aikata sun fara shiga jami’ar a yau inda suka bayyana farin cikinsu tare da fatan za a fara daukar darasi.
Kungiyar dai ta ce ta rubuta wa hukumar jami’ar Bayero Kano cewa malaman sun dawo bakin aiki.
Yayin da malaman jami’ar suka janye wannan yajin aiki, ga alama, shirye-shirye sun kankama na ci gaba da daukar darasi a Jami’ar Bayero Kano.
Bayanai sun ce an bude sashe-sashe na jami’ar da kuma dakin karatu a yau Litinin, inda ya tarar ana share-share da goge-goge.