✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’ar Ahmadu Bello za ta shawo kan rigingimun manoma da makiyaya

Cibiyar Bunkasa Binciken Dabbobi ta kasa dake Shika a Zariya (NAPRI) ta gudananar da taron gamayyar kungiyoyin manoma da makiyaya da masu fataucin dabbobi, inda…

Cibiyar Bunkasa Binciken Dabbobi ta kasa dake Shika a Zariya (NAPRI) ta gudananar da taron gamayyar kungiyoyin manoma da makiyaya da masu fataucin dabbobi, inda ya gudana a babban dakin taro na Kongo a makon da ya gabata. 

An gudanar da taron ne a karkashin jagorancin shugaban gudanarwa na Jamia’ar Ahmadu Bello, Iya Bayis Mashal Mukhtar Muhammad Wazirin Dutse (mai ritaya). Da yake jawabi a wajen taron ya bayyana cewa makasudin shirya wannan taron shi ne maida kungiyoyin manoma da makiyaya da kuma masu fataucin dabbobi ya koma na zamani, dan kawar da yawan fadace-fadacen da ake samu tsakanin manoma da makiyaya da kuma yawan samun dabbobi da ke addabar al’umma.

Haka kuma ya nuna farin cikinsa ta yadda kungiyoyin suka ba da goyon bayansu wajen halartar taron, tare da rokon da a sake shirya masu wani babban taron da ya fi wannan, domin kara wayar musu da kai.

Da yake nasa jawabin, Shugaban Cibiyar, Mista Clarence Ayodele Lalepine ya ce cibiyar ta samar da fili mai fadin hekta 600 domin samun hanyoyin da za a koyar da manyan kungiyoyin manoma da kuma makiyaya da masu fataucin dabbobi da kuma samar masu da kayayyakin aiki na zamani, “Mun kuma samu amincewar shugaban jami’ar Ahmadu Bello, Farfesa Ibrahim Garba na yin amfani da filin wanda ke harabar cibiyar, sannan ya yi mana alkawarin cikakken goyon bayan jami’ar ta yadda za a samar da nama da kwai da madara da kifi da kuma takin zamani ingantacce don samun cigaba a jihohinmu da kuma kasa baki daya.”

daya daga cikin mahalarta taron, kuma shugaban kungiyoyin mata ta Miyatti-Allah ta kasa, Hajiya Ladi Ardido ta jawo hankalin ‘yan uwanta Fulani da su bai wa wannan shirin goyon baya, kuma ta ce ya kamata iyayenta maza su rika kishin matansu wajen rage zuwa tallan nono da suke yi, wanda hakan ya sa tarbiyya da kuma kunyar da aka san su da ita ta gurbace. Sannan bukaci da su hada gwiwa da Jami’ar Ahmadu Bello domin zamanantar da sanar’ar tasu ta sayar da madara, a inda ta kawo misali da kanta cewar tunda take ba ta taba tallan nono ba duk da kasancewar an haife ta a ruga, amma ta samu ilimin zamani wadda kuma ta ke ganin amfaninsa.

kungiyoyin da suka halarci taron sun hada da kungiyar masu kiwon tumaki da awakai (MACBAN), Majalisar gamayyar kungiyoyin mata na Miyetti-Allah, kungiyar masu kiwo shanu na Miyetti-Allah (NASGODAN) da kungiyar masu kiwo da cinikin shanu ta Nijeriya, (CBDAN). Sauran su ne kungiyar samar da kayayyakin noma ta Najeriya (FACAN), Harsashin tunawa da Ahmadu Bello da kungiyoyin masu kiwon kaji na Najeriya (PAN) da kuma Hukumar samar da aikin yi ta kasa (NDE).