✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jami’ar ABU Zariya ta kori ma’aikata 15 masu laifi

Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zariya ta ragewa wani malamin jami’ar mukami tare da korar ma’aikata 15 sakamakon samun su da laifukan da suka hada da:…

Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zariya ta ragewa wani malamin jami’ar mukami tare da korar ma’aikata 15 sakamakon samun su da laifukan da suka hada da: kulla dangantakar yin alaka tsakanin ma’aikacin jami’ar da daliba da nufin yin lalata, da karbar rashawa tare sakaci wajen aiki.

Majiyarmu a yau Alhamis ta samu jerin sunayen wadanda aka kora daga tsangayoyin jami’ar daban daban.

Aminiya ta tuntubi Daraktan harkokin daliban jami’ar Dakta Sama’ila Shehu, ya tabbatar da korar ma’aikatan, wanda ya ce hakan zai zama darasi ga malamai da daliban jami’ar don kiyaye dokokin jami’ar.

Mahukuntar jami’ar sun yi zama na musamman kafin su zartar da hukuncin dokar korar ma’aikatan jami’ar.

%d bloggers like this: