✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’an tsaro sun ceto mutum 1 daga hannun masu garkuwa

’Yan banga, mafarauta da ’yan Amotekun ne suka yi ceton tare da ’yan sanda

’Yan sanda, jami’an tsaron Amotekun da mafarauta sun ceto daya daga cikin mutum biyu da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a ranar Kirsimeti a Jihar Ekiti.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 6 na yamma a kan titin Isan-Iludun, inda ’yan bindigar suka tsayar da matafiyan, sannan suka garkuwa da su.

Jami’an tsaro na ci gaba da kokarin ceto daya mutumin da aka yi garkuwa da shi.

Wata majiya daga Iludun a Ekiti ta ce, wata mota ce ta shaida wa jami’an ’yan sanda da na Amotekun cewar an yi garkuwa da wasu mutane a kan hanyar.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan jihar, Sunday Abutu, ya ce hadin guiwar ’yan sandan yankin Oye da wasu jami’an tsaro sun ceto mutum daya daga cikin wanda aka yi garkuwar da su.

Ya ce bayan samun rahoton faruwar lamarin, ’yan sanda, mafarauta, ’yan banga da jami’an Amotekun ne suka je wajen.

Kuma a cewarsa nan take suka yi nasarar ceto mutum daya, sannan suna ci gaba da kokarin ganin dayan ma an ceto shi.

Abutu ya ce nasarar da ’yan sandan suka samu ya nuna cewar yin aikin hadin guiwa da wasu jami’an tsaro zai taimaka wajen dakile muggan ayyuka a jihar.

Abutu ya ce, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Ekiti, Babatunde Mobayo ya bukaci al’ummar jihar da su ci gaba da taimaka wa jami’an tsaro bayanan sirri, don dakile ayyukan bata gari.