Sojoji sun bude wuta a kan masu zanga-zangar #EndSARS a kofar shiga birnin Legas da ke Lekki.
Jami’an tsaron sun bude wutar ne domin tarwatsa cincirindon masu zanga-zangar.
Bidiyon harbe-harben da masu zanga-zangar suka yada ya nuna sojojin suna harbi.
Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun ce an kashe mutum daya wasu da dama kuma sun jikkata.
Masu zanga-zangar sun ci gaba da gangamin nasu ne duk da sokar hana fita na awa 24 da gwamantin jihar ta sanya wanda ya fara aiki karfe 4 na yamma.
Suna tsaka da taron nasu a inda suka yi dandazon ne suka fara jin karar harbe-harbe, inda nan tare wurin ya hautsine kowa ya yi ta kokarin tsira.
Rahotanni sun ce sojoji sun yi wa wasu daga cikin masu zanga-zangar kawanya bayan mutanen sun kekashe kasa cewa su ba za su watse ba.
Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya dage lokacin farawar dokar da ya sanya zuwa karfe tara na daren ranar Talata.