✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jami’an lafiya 144 sun kamu da coronavirus a Kaduna

Ma’aikatan lafiya 144 sun harbu da cutar coronavirus a jihar Kaduna inda mutum 1,016 suka kamu da cutar tun farkon bullarta a jihar a watan…

Ma’aikatan lafiya 144 sun harbu da cutar coronavirus a jihar Kaduna inda mutum 1,016 suka kamu da cutar tun farkon bullarta a jihar a watan Afrilu.

Darektan Hukumar Bunkasa Lafiya a Matakin Farko ta jihar Dakta Iliya Neyu ya ce cutar ta kashe ma’aikacin lafiya guda daya daga cikin mutum 16 da ta yi ajalinsu a jihar.

“Zuwa yanzu mun sallami mutum 652 da suka warke, wasu 16 kuma sun rasu”, inji shi a jawabinsa ga taron manema labarai kan ayyukan kwamitin yaki da cutar coronavirus a jihar.

Iliya Neyu ya kuma ce mutum 348 na kwance a halin yanzu ana jinyar su da cutar a fadin jihar.

Jami’in ya bayyana cewa 76 daga cikin wadanda suka kamu da cutar a jihar yara ne, sai kuma mata 615 da maza 401.

Ya ce cutar ta bazu zuwa 15 daga cikin kananan hukumomin jihar, amma ta fi kamari a Kaduna ta Arewa inda mutum 305 suka kamu.