Dattawan Jihar Borno, sun zargi jami’an gwamnati da yi wa hukumomin tsaro kafar ungulu a yaki da ta’addanci.
Shugaban Kungiyar Dattawan Bonro, Farfesa Khalifa Dikwa ya ce manakisar da jami’an gwamnatin ke yi shi ne ummulhaba’isin ci gaban ta’addancin kungiyar Boko Haram.
- An cafke masu yi wa ’yan bindiga leken asiri a Neja
- An cafke Basarake da iyalansa kan zargin garkuwa da mutane
- ’Yan bindiga sun saki sabon bidiyon daliban Kwalejin Afaka
- Hada-hadar kudaden Cryptocurrency haramun ce —Sheik Bin Usman
“Suna yi wa sojoji da ’yan sanda makirci; duk da cewa jami’an tsaron sun taka rawar gani a wasu bangarorin da aka yi amfani da fasaha,” inji shi.
Da yake jaddada muhimmancin Najeriya ta rungumi amfani da fasahar zamani wurin yakar ta’addanci, Khalifa Dikwa, ya ce tilas ne gwamnatin Najeriya ta nemo kasashen da za su sayar mata da makamai, tunda wasu sun ki su sayar mata.
A hirar da gidan talabijin na Channels ya yi da shi, Shugaban dattawan Bornon ya ce, “Ya kamata Shugaban Kasa ya gano halin da tauraron dan Adam din Najeriya yake ciki.
“Shin tauraron dan Adam din zai iya dauko hotunan taswirar daga sararin samaniya? Shin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya za ta iya amfani da shi ba tare da an yi mata kutse ko katsalandan ba?
“Idan kuma ba mu da tauraron dan Adam din ne, to ya kamata ko na wata kasa ce mu karba aro.
“Amfani da fasaha na da muhimmanci, kuma jami’an tsaronmu za su samu nasara idan suna amfani da ita.
“Amma wasu jami’an gwamnati ke yin kutungwila ga amfani da fasaha? Alhali muna bukatar fasaha, sojoji na bukatar helikwaftoci masu gani a cikin duhu da sauransu; amma an ki a ba su.”