✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jami’an EFCC sun yi wa gidan Okorocha kawanya

Jami'an EFCC sun bukaci a turo musu karin ma'aikata, domin a su tafi da Okorocha

Jami’an Hukumar Yaki da Yi Wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC) sun yi wa gidan tsohon Gwamnan Jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha, kawanya.

A safiyar Talata ne jerin gwanon motocin EFCC dauke da jami’an hukumar suka yi dafafi a gidan tsohon gwamnan da ke lamba 3, Nyasa Close, daura da Layin Ontario, Maitama Abuja.

Majiyarmu a EFCC ta ce jami’an hukumar sun kai samame gidan Okorocha ne saboda ta sha neman shi don ya masa tambayoyi kan zargin almundahana, amma ya kin zuwa.

Wakilinmu da ya je gidan tsohon gwamnan a safiyar Talata ya lura ’yan sanda dauke da makamai suna karakaina a wajen.

Ya ce jami’an sun bukaci ta turo musu karin ma’aikata, domin a cewarsu, dole sai sun tafi da Okorocha.

Wakilinmu ya yi kokarin samu karin haske daga kakakin EFCC, Wilson Uwujaren, amma ko da ya kira wayansa bai dauka ba.

Karin bayani na tafe.

%d bloggers like this: