✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’a Ta Kafa Cibiyar Hada Magungunan Gargajiya A Gombe

Jami’ar North Eastern da ke Gombe ta bude cibiyar bincike da harhadda magungunan gargajiya da nufin samar da magunguna masu inganci da kuma aikin yi…

Jami’ar North Eastern da ke Gombe ta bude cibiyar bincike da harhadda magungunan gargajiya da nufin samar da magunguna masu inganci da kuma aikin yi ga daliban da ke kammala karatu ba tare sun aiki ba.

Shugaban Jami’ar mai zaman kanta,  Dokta Sani Jauro, Dan Lawan din Gombe, ya ce jami’ar ta kuma samar da cibiyar nazari da bincike kan tsirrai dan gano magungunan da suke yi da kuma yadda za a yi amfani da su.

Akwai kuma katafaren fili da jami’ar ke noma kowacce irin ciyawa da kuma itatuwa domin gano amfaninsu, wanda idan ba noma su ake yi ba za a neme su nan gaba.

Shugaban jami’ar ya sanar cewa jami’ar ta yi suna cikin shekara takwas da kafuwarta, kuma yana sa ran jama’a sun gamsu da ita.

Shi ya sa suka canja mata suna daga Pen Resource University zuwa North Eastern, ganin cewa a Arewa maso gabas take, domin komai nata ya tafi daidai da al’adu da tsarin Arewa.

A hirarsa da manema labarai bayan bikin sauya sunan jami’ar, Sani Jauro ya, daya daga cikin dalilan samar cibiyar magungunan gargajiya shi ne, samar da aikin yi ga dalibai tun kafin su gama jami’a saboda yanzu aikin gwamnati ba ya samuwa.

Akwai kuma wajen koyar da sana’oi daban-daban, kamar harhada magungunan gargajiyar da sauransu wanda idan dalibi ya kammala karatu zai dogara da kansa.