Gwamnati a Jamhuriyyar Benin ta tsawaita wa’adin tsare mutumin nan mai rajin kare hakkin Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho da watanni shida a Cotonou, babban birnin kasar.
Wannan dai na cin karo da sanarwar da wani lauya mai kare hakkin bil Adama da ke Abuja, Pelumi Olajegbesi ya yi a karshen makon da ya gabata cewa za a saki Igboho nan ba da jimawa ba.
Sai dai da yake martani kan sanarwar da aka fitar a ranar Lahadi, lauyan Igboho, Yomi Aliyu ya ce gwamnatin Jamhuriyyar Benin ta sabunta wa’adin tsare wanda yake wakilta ne na tsawon watanni shida duk da cewa ba a tuhumarsa da aikata wani babban laifi kuma babu wata bukata da aka shigar ta taso keyarsa zuwa Najeriya daga gwamnatin kasar.
Aminiya ta ruwaito cewa, tun a watan Yulin 2021 ne Sunday Igboho ya shiga hannu bayan jami’an tsaron kasar da ke yankin Yammacin Afirka suka yi ram da shi a filin jirgin saman Cotonou yana kokarin guduwa Jamus.
Tun a farkon watan Yulin bara ne dai Hukumar Tsaro ta DSS ta ayyana Igboho a matsayin wanda take nema ruwa a jallo bayan wani samame da ta kai gidansa.
Bayanai sun ce wata kotu ce dai a Benin ta bayar da umarnin a kai jagoran masu fafutikar kafa kasar Yarbawa a Najeriya gidan yari da a yanzu ya shafe fiye da kwanaki 200 a tsare bayan ’yan sandan kasar sun cika hannunsu da shi.
Ana iya tuna cewa, Sunday Igboho ya tsere daga kasar nan bayan da aka kai samame gidansa kuma hukumomin tsaro suka yi ikirarin samun tarin makamai da ya boye.