✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

James Rodriguez ya koma Bayern Munich

Dan kwallon kulob din Real Madrid na Sifen James Rodriguez a ranar Talatar da ta wuce ne ya tabbatar da canza shekarsa daga kulob din…

Dan kwallon kulob din Real Madrid na Sifen James Rodriguez a ranar Talatar da ta wuce ne ya tabbatar da canza shekarsa daga kulob din zuwa na Bayern Munich da ke Jamus a matsayin aro.

Dan kwallon ne da kansa ya sanar da wannan labari a shafin sadarwasa ta Instagram inda ya nuna ya rattaba hannu ne a kwantaragin shekara biyu ga kulob din Bayern Munich na Jamus a matsayin aro.

James, dan shekara 25, ya koma kulob din Madrid ne daga na Monaco ta Faransa a shekarar 2014 bayan an kammala Gasar Cin Kofin Duniya da ta gudana a Brazil bayan ya zama dan kwallon da ya fi yawan zura kwallaye a gasar.

Sai dai tun bayan da Kocin Madrid Zinedine Zidane ya karbi ragamar horar da kulob din ya nuna James bai yi masa ba, hasalima ba shi daga cikin ’yan kwallon da yake amfani da su a kowane lokaci da hakan ta sa dan kwallon ya nemi barin kulob din kafin a fara kakar wasa ta bana.

A da an dauka dan kwallon zai koma kulob din Manchester United ko na Chelsea ne a Ingila sai ga shi ya yi ba-zata ya koma kulob din Munich don ci gaba da kwallo.