Shugaban Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu ta Kasa (JAMB), Farfesa Ishaq Oloyede ya ba da umarnin kada a sake barin iyayen yara masu rakiya su shiga dakunan jarabawar.
Ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da kakakin ofishin hukumar dake Ilorin a jihar Kwara ya fitar ranar Juma’a.
- ‘’Yan bindiga na barazanar mayar da ’ya’yanmu matansu’
- Turkiyya ta haramta amfani da kudaden Cryptocurrency
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa shugaban ya bayyana hakan ne lokacin da ya je domin duba wata cibiyar yin rijistar jarabawar a jihar Kwara amma ya tarar da su ba matsaka tsinke.
Sanarwar ta kara da cewa, “Shugaban ya ce sun gano cewa iyaye ne a ko da yaushe ke kawo cunkoso a cibiyoyin tare da rashin bin matakan kariya daga cutar COVID-19,” inji Farfesa Oloyede.
Daga nan sai ya shawarci iyaye da ma wakilansu da su daina yi wa ’ya’yan nasu tsallaken ajin da ya wuce kima.
“Alal misali, mai shekaru 14 ko 15 bai yi hankalin da zai jure fadi-tashin neman gurbin karatu a jami’a ba, kuma zai iya fadawa hannun ’yan damfara a kowanne lokaci,” inji shi.
Farfesa Oloyede ya kuma shawarci ma’aikatun ilimi da sauran masu ruwa da tsaki da su tabbatar da cewa sun gano hakikanin shekarun dalibai kafin ma su yarda su dauke su a makarantun sakandire.