✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

JAMB ta dora laifin kashi 80% na matsalar rijista kan dalibai

JAMB ta nuna damuwa kan yadda daliban suka gaza bin ka’idojin rajistar da ta gindaya.

Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu ta Kasa (JAMB) ta ce fiye da kashi 80 cikin 100 na matsalolin da daliban da ke son rubuta jarrabawar UTME da DE ke fuskanta yayi rijista a bana su suka ja wa kansu.

Shugaban hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede ne ya bayyana hakan yayin da yake aikin duba wadansu daliban da za su rubuta jarrabawar a cibiyoyin Kogo-Bwari da Garki da ke Abuja wadanda suka gaza yin rajistar har aka rufe.

Ya nuna damuwa kan yadda daliban da dama suka gaza bin kananan ka’idojin rajistar da hukumar ta gindaya, yana mai cewa fiye da kashi 80 na kalubalen da aka samu daliban ne suka haifar da su.

Ya ce, “Galibinsu sun aika abubuwan da ba daidai ba a matsayin Lambar Shaidar Zama Dan Kasa ta NIN, da hakan ya sanya hukumar NIMC ta kasa tantance lambobin nasu.

“Daliban ne suka haddasa wa kansu matsalolin. Ko dalibi yana aika sakon kar ta kwana domin rijistar kundinsa amma ba shi da N50 a layin wayarsa,” inji Farfesa Ishaq.

Shugaban ya ce hukumar tana aikin ne domin ire-iren wadannan daliban su bayyana korafe-korafensu kan kalubalen da suka fuskanta musamman wadanda suka ce ba su da lambar ta NIN gaba daya ko kuma sun same ta a makare.