✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

JAMB ta ba da kyautar N375m ga Jami’o’i 5 mafiya kwazo a Najeriya

Hukumar JAMB mai shirya jarrabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandire a Najeriya, ta bayar da kyautar Naira miliyan 375 ga wasu jami’o’i guda biyar…

Hukumar JAMB mai shirya jarrabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandire a Najeriya, ta bayar da kyautar Naira miliyan 375 ga wasu jami’o’i guda biyar da suka fi sa’o’insu kwazo a kasar.

Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu ne ya bayyana hakan a yayin taron bayar da lambar yabo ga manyan makarantun gaba da Sakandire mafi kwazo a bara wanda hukumar JAMB ta gudanar karo na biyu kenan a birnin Abuja.

Malam Adamu ya ce wannan yana daya daga cikin tsare-tsaren fidda gwarazan jami’o’i da Gwamnatin Tarayya ta shirya ga manyan makarantun gaba da sakandire domin ramawa kura kyakkyawar aniyyarta tare da basu tallafi.

“A shekarar 2019, Hukumar JAMB yayin kaddamar da shirin a karon farko, ta baiwa manyan makarantun gaba da sakandire da suka ciri tuta tallafin naira miliyan 125, kuma a wannan karo ta bayar da tallafin naira miliyan 375 wanda babu shakka kyakkyawar manufa ce wacce ta cancanci kwaikwayo,” inji Ministan.

Jami’o’in guda biyar da suka zama zakaru a rukunai biyar daban-daban na samun lambar yabo wanda Hukumar JAMB ta fitar, kowannensu zai su samu kyautar naira miliyan 75.

Ministan yayin da yake taya manyan makarantun murnar samun wannan nasara, ya kuma kalubalanci sa’o’insu da suka zo na biyu da suka kara jajircewa a karo na gaba.

A yayin da yake zayyana sunayen jami’o’in da rukunan da suka yi zarra, Shugaban Hukumar JAMB, Farfesa Is-haq Oloyede, ya ce Jami’ar Ilorin ita ce jami’ar da dalibai suka fi rububin neman samun guraben karatu a bara, yayin da Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta yi wa sauran fintinkau wadda ta zamto Cibiyar bayar da guraben karatu ga dalibai ta Kasa.

Ya ce Jami’ar Tarayya ta Wukari ta lashe kyautar Cibiyar Ilimi mafi Inganta daidaito a tsakanin jinsin Maza da Mata, yayin da Jami’ar Ilorin ta kuma sake lashe lambar yabo ta Jami’ar da ta fi kowacce baiwa daliban kasashen ketare mafi yawa guraben karatu.

Kazalika, ya ce Babbar Cibiyar Koyar da Fasaha ta Jihar Ogun da ke Igbese, ta ciri tuta a matsayin cibiyar ilimin da ta fi kowacce tabbatar da kiyaye ka’idodi wajen baiwa dalibai guraben karatu.

Farfesa Oloyede ya ce ana tsammanin wannan manyan makarantu za su yi amfani da kyautar kudin da suka samu wajen gine-ginen tituna a cikinsu.