’Yan sanda sun cafke wani kasurgumin dan fashi da ya addabi yankin Nnewi na Jihar Anambra dauke da bindigar Pistol kirar asali.
Jami’an sun damke Chiemezie Kenneth Aligu shekaru 24 wanda ake nema ruwa a jallo, wanda dan asalin Jihar Ebonyi ne.
- Gwamnati ta rage kudin mai
- Maryam al-Balushi: Matar da ke kiwon kyanwoyi 480 da karnuka 12 a gidanta
- Jibge jami’an tsaro awa 24 a hanyoyi zai magance satar mutane —Matasa
Kakakin ’yan sandan Jihar, SP Haruna Mohammed ya ce tun da farko rundunar samu kiran waya cewa dan fashin ya yi kwacen wata mota kirar Honda CUB50 a yankin Okpuno Otolo da ke Karamar Hukumar Nnewi.
Nan take aka tashi ’yan sanda a Karamar Hukumar Nnewi na Otolo tare da hadin guiwar ’yan bangar Egbumuenem da na Otolo su hanzarta kai samame su cafke wanda ake zargin.
Jami’an ba su yi wata-wata ba, suka garzaya zuwa yankin inda suka dana wa dan fashin tarko, kafin ya ankara sun yi masa kofar rago sun cafke shi.
Jami’in ya ce an kama dan fashin yana dauke da bindigar Pistol kirar asali mai lamba 941396, wayoyin tarho guda biyu da babur din hawa.
Ya kara da cewa fusatttun mazauna yankin sun yi wan dan fashin dukan kawo wuya har ya fadi magashiyan kafin ’yan sanda suka dauke shi suka wuce da shi zuwa asibiti.