✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jadawalin gasar cin kofin Afirka da za a yi badi a Kamaru

Tawagar Super Eagles tana rukuni na hudu a gasar da za a fafata a Kamaru.

A ranar Talata ce Hukumar Kwallon Kafar Afrika ta fitar da jadawalin gasar cin kofin nahiyar wato CAF wanda Kamaru za ta kasance mai masaukin baki a wannan karon.

Gasar ta Africa Cup of Nations na kunshe da kasashe 24 wadanda aka rabasu zuwa rukunnai shida kowanne dauke da kasashe hudu-hudu.

Kamar yadda yake bisa ala’ada, kasashen 24 za su shiga rukunnansu ne bisa la’akari da matsayinsu a matakin kwarewa da FIFA ke fitarwa.

Gasar da ta kunshi kasashe 24 za a fitar da gwanaye biyu a kowanne rukuni wato wadda ta yi ta daya da ta biyu kenan.

Za kuma a hada da tawagogi hudu da suka yi na uku-uku da maki mai kwari, domin kai wa zagaye na biyu a wasannin.

Bayanai na nuna cewa taron fitar da jadawalin gasar da ya gudana a Kamaru, ya samu halartar manyan-manyan ’yan wasan nahiyar ta Afirka ciki har da Samuel Eto’o da Didier Drogba da Yaya Toure da kuma Austin Jay Jay Okocha.

Za dai a fara da bikin bude gasar da karawa tsakanin Kamaru da Burkina Faso ranar 6 ga watan Janairu da ake sa ran karkare wa a ranar 9 ga watan Fabrairun badi.

Cikin jadawalin da aka raba ranar Talara a Yahounde, Tawagar kwallon kafa ta Najeriya wato Super Eagles wadda ta ci kofin karo uku, tana rukuni na hudu a gasar da za a fafata a Kamaru.

Jadawalin na CAF na nuna cewa rukunin farko wato A na dauke da kasashen Kamaru mai masaukin baki, kana Burkina Faso da Habasha da kuma Cape Verde.

Sai rukunin B da ya kunshi Senegal jagorar kwallon kafa a Afrika, sai Zimbabwe da Guinea da kuma Malawi.

Akwai rukunin C da ke kunshe da kasashen Morocco da Ghana da tsibirin Comoros da kuma Garbon.

Sannan rukunin D wanda ke dauke da Najeriya da Masar da Sudan da kuma Guinea Bissau.

Rukunin E na gasar na kunshe da Algeria mai rike da kambu da Sierra Leone da Equatorial Guinea da kuma Cote D’Ivoire.

Sai kuma rukunin karshe na F da ke dauke da kasashen Tunisia da Mali da Mauritania da kuma Gambia.

Tun a 2019 ya kamata Kamaru ta karbi bakuncin gasar kofin Afirka, amma ta kasa kammala shirye-shiryenta da ya sanya aka bai wa Masar damar karbar bakuncin wasannin.

Hukumar CAF ta sake bai wa Kamaru izinin karbar bakuncin gasar a 2021, amma annobar cutar Coronavirus ta janyo tsaikon da aka dage wasannin zuwa 2022.

Ga Jadawalin gasar cin kofin Afirka da za a yi badi a Kamaru:

Rukunin farko A: Cameroon, Burkina Faso, Ethiopia, Cape Verde

Rukuni na biyu B: Senegal, Zimbabwe, Guinea, Malawi

Rukuni na uku C: Morocco, Ghana, Comoros, Gabon

Rukuni na hudu D: Nigeria, Egypt, Sudan, Guinea-Bissau

Rukuni na biyar E: Algeria, Sierra Leone, Equatorial Guinea, Ivory Coast

Rukuni na shida F: Tunisia, Mali, Mauritania, Gambia