✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jacob Zuma ya sha da kyar

Shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya sha da kyar a kuri’a ta baya-bayan nan da ‘yan majalisar dokokin kasar suka kada domin tsige…

Shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya sha da kyar a kuri’a ta baya-bayan nan da ‘yan majalisar dokokin kasar suka kada domin tsige shi daga kan mulki.

BBC ta ruwaito cewa ‘yan adawa sun yi fatan cewa kada kuri’ar a sirri zai sa ‘yan majalisar jam’iyyarsa ta ANC su juya masa baya.

Sai dai a kuri’ar, wacce aka shirya saboda zargin cin hanci da ake wa shugaban, ya samu rinjaye da 198 yayin da ‘yan hamayya suka samu 177.

‘Yan majalisar jam’iyyarsa ta ANC sun barke da murna lokacin da aka sanar da sakamakon kuri’ar.

Ana bukatar ‘yan jam’iyyar ANC akalla 50 daga cikin 249 su juya wa shugaban baya kafin a iya tsige shi.

Sai dai sakamakon ya nuna cewa akalla ‘yan ANC 26 ne suka juya wa shugaban baya, yayin da tara suka kaurace wa kuri’ar.

Tun da farko shugabannin adawar sun yi gargadin cewa Afirka ta Kudu za ta kama hanyar “mutuwa” idan har Shugaba Zuma ya tsallake kuri’ar.

 

…Yan jam’iyar ANC sun yi zurfin tunani – Dokta Bala

Dokta Bala Muhammad, malami a Jami’ar Bayero ta Kano da ke Najeriya a zantawar sad a BBC, ya ce ‘yan jam’iyar ANC da ke majalisar ne za su gwammace kida da karatu muddin suka sa aka tsige shugaba Zuma.

“Idan suka sa aka cire Zuma mecece ribarsu?, kuma ina aka dosa, idan suka cire shi ba su san abin da zai biyo baya ba.’’ In ji shi.

Dokta Bala Muhammad ya kara da cewa da alamu sun nuna cewa ‘yan majalisar sun yi duban hankali ne daga bisani, suka ga cewa idan suka sake aka cire Zuma su ne za su fi tafka asara.

“Watakila sun yadda da dukkan abin da ake fada na laifin Jacob Zuma, amma kuma suna duba cewa idan aka cire shi aka samu hargitsi a jam’iyar za su samu koma baya’’, in ji masanin.

Tun da farko shugabannin adawar sun yi gargadin cewa Afirka ta Kudu za ta kama hanyar “mutuwa” idan har Shugaba Zuma ya tsallake kuri’ar.