✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ja-in-jar jan-janin Janye-wuri

Jan-janin janye wuri dan kwadago da na-mujiya wuri-wuri Matsaloli sun sa an yi kuri Jiki na hajijiyar jin jiri Ko kwanyara kukan jinjiri   Dankari…

Jan-janin janye wuri

dan kwadago da na-mujiya wuri-wuri

Matsaloli sun sa an yi kuri

Jiki na hajijiyar jin jiri

Ko kwanyara kukan jinjiri

 

Dankari makari

Da hunturu an fito firi-firi

Kar ku ganni a firgigi

Haurobiyawa ban da walagigi

Lallai za a kwance mana sasari

 

Baba yai mana tari

Na dan yi mura da tari

Mai ingarma ba ya hawa kuturi

Miyagu sun sa a na jan kari

Ta’asa sai an kaita kabari

 

Jayayyar juyin shekara

Jan-ragamar mai fikira

Fuffukar-fuka-fukin fakara

Farantin taliyar cin tara

Fafutikar takarar taka-kara

 

Jan dagar jarumi

Na-raye da na-mujiya yai arba

Nagartar mutum mutu ka raba

Jinkirin rabon mukami

Rudanin masu bambami

 

Dubun karamin laujen silin magirbi

Baba ya zare takobi

Zai sauke kurungun ayyukan aibi

Mu dai mu yi dabgen zabi

A hada mana kulorar jangahur da zabibi

 

Gayauna za ni da masassabi

Tuni na warware daga zazzabi

Na daina jin zafi a kwibi

Ku taho kowa ya bi

Garkar gayauna labi-labi

 

Giringidimin gangarowar Girigogriya

Gagarumar shekara

Gagara-kuwar ’ya’yan asara

Gagarabadau daura aniya

Gurguri goribar gwagwarmaya

 

Tattalin tulin dukiya

Mai na-duke da kiwon tunkiya

Gayauna tai yabanya

Uwargida sanye da abaya

Na ga maigida da jallabiya

 

Ai wa kasa sutura takamala

Aikin ingata ra yuwa ya malala

Gayauwna mun bar wasu na ta kala

Mui watsi da masu takala

Makirai an tsala musu bulala

 

Tun farkon Hijiriya

Kyawawan dabi’u ake ta bibiya

Ha mu a sabuwar Girigoriya

Gasuwar Baban-buron-huriyya

A daina duk wata dirkaniya

’Yan kasa za su yi dariya

 

Garar dabgen dadin duniya

Girkin ga hada da tsuntsun miya

A damo kunun tsamiya

Gasarar koko a kwatanniya

A kandamo gudajin gaya

 

Jalli-jogar janjalo

Hallo alalo

Sidddabarun dabara salo-salo

Ka shige cikin gwalalo

Ka yi wa jama’a gwalo 

 

Bayan kowace wahala

Da ta haifar da lalala

Jikin wasu yai kasala

Har wasu sun hassala

Da hutu sai a taba dafdala

 

Gargadin gudun gara

In an fada zago an makara

A zo ana neman kakara

Al’umma a daina kagara

Mu kara kaimi kowa ya zabura

 

Farko zuwa karshen shekara

An samu dimbin al’amura

Wasu sun faskara

Bara-gurbi sun yi wasan dara

Da walwalin waliyon mashillara

 

Ja-in-jar Janye-wuri

Fankamar Farin-biri

Marisar marmari

A-farin-lilon wata nagari

Mayun-miyagu a garari

 

Yawon-wuni

Yawon-wulli

Agusata na ruwan tulu tuli

Sautun-tumun-Baba babu balli

Ukkun-toton Baba mai iyali

 

A zo Noman-Baba

karshe dai Dashen-Baba

Ai ta sakar tabarmar kaba

A kiyayi jagaliyar ’yan daba

A kiwo an kora ’ya’yan dabba

 

Tabbacin rashin tababa

Haurobiyawa a daina gaba

A kiyayi giba

Mu hau bisa kyakkyawar turba

A  girgoriya mu kara samun tsaba

 

Sabanin yadda haurobiyawa suka saba yi wa juna fatan alheri da adu’o’i nagari duk sa’adda aka NAUYAYYA-NIYYAR sabuwar shekara ta HIJIRIYYA ko GIRIGORRIYA, wannan karo sai aka karke da JA-IN-JAR JANYE-WURI da JAN-JANIN-JAN-NA-MUJIYA yai kURI, wai saboda Baban-burin-huriyya ya bai wa matattu mukami. Wannan lamari ai ta kwana gidan sauki, domin faduwar wani tashin wani, sai a daina duk wani wuni-wuni.

Mu kauce wa kwaramniya, musamman masu neman kamuya-muya a sabuwar shekarar Girigoriya, don ya zama dole mu gwagwiyi goribar gwagwarmaya, don kada a yi mana mamaya. Farkon wata dai ya tsaya.

Baba dan Adam ne na  san yana kuskure, amma bai cika yin ganganci ba, musamman kan al’amarin da ya shafi jan ragamar al’ummar kasa, tunda ai yana so kowa ya warwasa, mu ci WASA-WASA. Kuma ko a farfajiyar wannan katafariyar makaranta mun sha bijiro muku da batun yadda za a kwashi KWALAM da MAkWALASHE, mu ce wa miyagu CIN-BIM-kWALAM!

Batu na ingarman karfen karafa, muna fatan ganin Baba ya samu galaba a kan masu karfa-karfa da suke yi mana fafa, wadanda aikinsu ya zafafa, musamman yadda a dukan ta-mola suke fafutikar ganin sun zarta FIFA!

Baba kura ta lafa, amma kada a yi wasararai da tsillin matsala kodabata wuce kan akaifa ba. Ba za mu lamunce da kowace kutungwila da ke sanya al’umma ta hassala ba. Mu yi hadakar hadin gwiwar karfen karafan kwangiri titin taragon dogo a daukacin lokacin wulwulawar agogo ta yadda za mu tuinkari mai kilago mu tamke shi da da bawon kalgo, Baba ne dai babban jigo  wannan balaguro don haka na raba muku marsa goriyar goro. Kow aya samu hoto ku zo mu yi taro, ta yadda in jinbirin wake ya nuna babu wanda zai kasala a wajenm roro.lallai mun JIMIRI DA JINKIRIN CIN JINbIRI!

Ni  dai shawarata Baba da sauran managarta mutanen da ke jan-ragamar al’umma lallai su daina kula jam’iyya mai dan boto da sanda jirge, domin ba su da wani katabus, tunda an kawo karshen camamar cin cammas da cin CUKUBUS su yi ta tusa tus-tus!

Baba da Inna lallai a dauki tsintsiya a share mana jiba da daukacin kazantar tsilli-tsillin matsalolin da suka dabaibaye Haurobiya, ta yadda kowa sai ya yi dariya, sannnan mu himmatu ka’in da na’in wajen kyautata tunani da agaza wa juna. Mu yi kishin kasa ban da KISSA da KISISINAR KISHIYA, al’amarin da ke haifar mana jibga wa juna JIbAR TSIYATAKU, Haurobiyawa Gwamnati ta sauya managarcin SALON KIdA lallai sai mu sauya TAKU!