✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Izala ta kaddamar da masallacin Juma’a a Kasuwar Maliya

kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS) ta kaddamar da masallacin Juma’a da aka gina a kasuwar dabbobi ta Maliya da ke kan hanyar…

kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS) ta kaddamar da masallacin Juma’a da aka gina a kasuwar dabbobi ta Maliya da ke kan hanyar Abuja zuwa Keffi, a yankin karamar Hukumar Karu ta Jihar Nassarawa.

Masallacin wanda wani bawan Allah ya gina tare da bai wa kungiyar don gudanarwa, an kaddamar da shi ne a ranar Juma’a da ta gabata, inda malamai da sauran shugabannn al’umma suka halarta tare da gudanar da wa’azi.

A wa’azin da ya gabatar, daya daga cikin malaman da suka gabatar da nasiha a yayin taron mai suna Malam Muhammad Jamil Sulaiman, ya hori al’ummar Musulmi da su gabatar da wani aiki na alheri a rayuwarsu irin masallaci don samun ladansa ko bayan mutuwa; inda ya ce Allah Ya yi alkawarin gina gida a cikin aljannah ga duk wanda ya gina masa masallaci.

Shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, Alhaji Bello Abdullahi Bodejo ya bayyana farin ciki a kan aikin sannan ya bayyana godiya ga wadanda suka halarci taron.

A hudubarsa ta farko, limamin masallacin Sheikh Idris Ibrahim Alfalati ya bukaci hadin kan al’ummar Musulmi a kan tafarkin sunnar Manzon Allah (saw) tare da neman ilimin addini da na sauran fannoni. Ya yi addu’ar sakayya da gidan aljannah ga wanda ya gina masallacin, sannan ya bukaci al’ummar yankin da su ba da hadin kai wajen raya shi.

Sarkin fawan Abuja Alhaji Usman da kuma shugabannin al’umman makiyaya daga wasu jihohin kasar nan, na daga cikin wadanda suka albarkaci taron.