✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iyayen mutumin da ake tuhuma da kashe Hanifa sun tsere

Iyayen Abdulmalik Tanko sun cika bujensu da iska babu shiri.

Iyayen Abdulmalik Tanko, mutumin nan da ake tuhuma da kisan yarinyar nan ’yar shekara biyar, Hanifa Abubakar, sun tsere daga matsuguninsu saboda barazanar kai musu hari.

A ziyarar da Aminiya ta kai Unguwannin Tudun Wada da Tudun Murtala a Jihar Kano, wadanda nan ne matsugunar Abdulmalik Tanko, makwabta sun bayar da shaidar cewa ba su da masaniyar inda iyayensu suka shiga.

Makusanta sun bayyana cewa, aika-aikar da Abdumalik ya yi ce ta janyo a bayan nan aka rika kokarin kai wa iyayensa hari, lamarin da ya sanya suka tsere daga gidansu babu shiri.

Wani da ya bayar da sunansa a matsayin Musa Shehu, ya ce, “a halin yanzu babu wanda zai fadin hakinanin inda iyayen Abdulmalik suka shiga, sun sauya sheka.

“A halin da ake ciki ma mahaifiyarsa ta ki karbar rikon ’ya’yansa, inda har ta kai ga ta ce babu wata alaka da ke tsakaninsu kuma a yanzu.”

Tuni dai Aminiya ta ruwaito cewa, Abdulmalik Tanko, mamallakin makarantar Nobel Kids Academy a Jihar Kano, ya amsa cewa shi ya kashe Hanifa ta hanyar dura mata shinkafar bera.

A ranar Litinin ce dai Abdulmalik Tanko wanda shi ne malamin makarantar da ake tukuma da garkuwa da kuma kashe dalibarsa ’yar shekara 5 ya bayyana a gaban kotu karon farko.

Aminiya ta ruwaito cewa, Abdulmalik ya bayyana gaban kotun ne tare da mutane biyu, Hashimu Ishiyaku, da Fatima Jibrin Musa da ake zargi suna da hannu a garkuwa da kuma mutuwar Hanifa.

Tun a farkon watan Disamban bara ne aka sace Hanifa lokacin da take kan hanyar komawa gida daga makarantar Islamiyya.

Malamin dai ya bukaci a biya shi Naira miliyan shida a matsayin kudin fansarta, inda a wajen karbar kudin ne dubunsa ta cika.

Sai dai ko a lokacin da yake kokarin karbar kudin fansar ma ya riga ya hallaka ta, amma ya ki shaida wa iyayenta.

To sai dai bayan kama shi, wanda ake zargin ya shaida wa ’yan jarida a hedikwatar ’yan sandan Kano cewa da shinkafar bera na N100 ya yi amfani wajen kashe yarinyar.