✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iyayen Ese Oruru sun yi zargin za a sace masu jika

Tun bayan bayyanar takaddama a tsakanin iyayen Ese Oruru da  Yunusa dahiru, wanda ake wa lakabi da Yellow, wata shida da suka gabata; sai ga…

Tun bayan bayyanar takaddama a tsakanin iyayen Ese Oruru da  Yunusa dahiru, wanda ake wa lakabi da Yellow, wata shida da suka gabata; sai ga shi kwatsam wata sabuwa na neman tasowa, inda iyayen suke zargin wadansu mutane da ba a san ko su wane ne ba da yunkurin sadadawa gidansu, da nufin sace jikarsu, wadda ko wata hudu da haihuwa ba ta cika ba.
Iyayen yarinyar da ke cikin halin damuwa, sun gana da manema labarai a Yenagoa, suka shaida musu halin da suke ciki, inda suka ce: “A nan inda muke da zama a harabar barikin ’yan sanda, mun lura wadansu mutane bakin fuska suna yawan zuwa suna duba gidan da muke, har ma wani muka gani yana yin waya da harshen da ba mu fahimta. Daga bisani sai aka gaya mana cewa mutumin yana cewa ai ya gane gidan da take. Hakan ya yi matukar tayar mana da hankali. Sai muke zargin ko ana so ne a dauke mana jika zuwa wani wuri na daban da ba mu sani ba,” inji ’yan uwan Ese.
Haka kuma sun ce sun sanar da Rundunar ’Yan sandan Jihar Bayelsa game da lamarin, musamman lura da yadda aka rage yawan jami’an tsaro da ke ba su kariya a gidansu.
Da aka tuntubi mai magana da yawun Rundunar ’Yan sandan Jihar Bayelsa, Mista Asinim Braithwight game da lamarin, ya ce zuwa yanzu rundunarsu ba ta karbi wani korafi daga gidan su Ese ba.