Iyayen wani dalibin makarantar sakandare sun dauki hayar ’yan daba suka lakada wa malamin dansu nasu dukan kawo wuka a makarantar.
’Yan dabar da iyayen daliban sun farmaki malamin ne saboda duka da ya yi wa dansu wanda ke ajin karshe a makarantar sakandare ta Toyon High School da ke kauyen Ere a Karamar Hukumar Otta a Jihar Ogun.
- Gobara ta kashe mutum 6, wasu 17 sun jikkata a birnin Valencia
- NAJERIYA A YAU: Shin Ya Dace Malaman Addini Su Shiga Siyasa?
An cafke ’yan dabar da suka yi wa malamin aika-aika a ranar Talata, bayan samun kiran agaji da Rundunar ’Yan Sandan jihar ta yi a ofishin ’yan sanda na Ado-Odo.
Kakakin ’yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da cafke ’yan dabar, inda ya ce su ma iyayen dalibin sun shiga hannu.
Oyeyemi ya shaida wa manema labarai cewar dalibin ya yi laifi ne kamar yadda malaminsa ya bayyana, kuma ya hukunta shi, amma da ya koma gida ya sanar da iyayensa cewar malamin ya masa dukan kawo wuka, wanda hakan ya fusata su.
“’Yan dabar sun fasa gilashin wata mota mai dauke da lamba LSD 395 FV, mallakin wani malami.
“Malamin ya ji rauni amma an kai shi asibiti don ba shi kulawa.
“Kwamishinan ’yan sandan jihar, Lanre Bankole, ya bada umarnin cafke ragowar wadanda suka tsere don gurfanar da su gaban shari’a,” a cewar kakakin.