✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iyaye nagari ginshikin samun managarciyar al’umma

Alhamdulillahi, wassalatu wassalamu alal khairul huda, sayyadina wa wahabibuna Muhammad (SAW).Assalamu Alaikum ma’abota bin wannan fili mai farin jini. Zan dauki bangarori guda uku da…

Alhamdulillahi, wassalatu wassalamu alal khairul huda, sayyadina wa wahabibuna Muhammad (SAW).
Assalamu Alaikum ma’abota bin wannan fili mai farin jini.
Zan dauki bangarori guda uku da rashin samun kamalar su ko ingancin su, kamar yadda tsarin musulunci da al’adunmu suka tanadar, sai ka ga an kasa samun al’umma na gari.
Sune kamar haka;
1-IYAYE,
2-MALAMAN MAKARANTU (ARABI DA BOKO),
3-GWAMNATI.
A cikin bayanin, in na ambaci al’umma ina nufin matasa don su ne ake tokabo da su yayin da suke managartaddu, kuma abun tir in aka samu akasin hakan.
Sanin kowa ne, iyaye sune mataki ko in ce makaranta ta farko da yara ke ratsawa, in muka duba, an ce namiji ya nemawa ‘ya’yan sa uwa tagari, haka mace ta nema wa ‘ya’yanta uba na gari.
Na daga ciki umurnin ma’aiki SAW da ya  ce “ku zabi ma’abociyar addini”, “shi kuma namiji wanda kuka yarda da addininsa da dabi’u kyawawa”.  Ya zamu gaskata wannan?
Sai mu duba tun wajen neman auren an bi shari’a?, wajen saduwa fa?, Renon cikin fa?, Haihuwar sa har zuwa shayarwa?,
Kama zuwa renon sa har ya fara zama da tafiya, har ya kai minzalin fara tafiya karshe ya fara zuwa makaranta, duk ana bin sharudda da ka’idojin islama?, Ta yaya za’a samu hakan?,
Sai da ilimi, to wannan ya rage mu je mu durkusa gaban malamai masu tsoron Allah don neman rabauta duniya da lahira. Kun ga kenan zaben iyaye na gari tun farkon neman aure shine mataki na farko.
Wa za ka/ki aura?,
Duk ba sai na koma baya ba malamai da dama sun yi bayanai, amma abin sani shi ne uwa ita ta kwashe kusan kaso 70 cikin 100 na tarbiyya, kuma in har aka yi rashin sa’a ba ka samu mace ta gari ba to fa tunda safiyar rayuwarku gidanka ya lalace, kuma abin takaici zai harbi sauran al’umma.
(MALAMAN MAKARANTU (ARABI DA BOKO) GINSHIKAN SAMUN AL’UMMA TA GARI).
Kamar yadda na fada a baya, iyaye su ne makaranta ta farko da yara ke bi kafin su fara fita waje.
Duk kokari da iyaye za su yi wajen tarbiyantar da yaran su, in ba a samu malamai masu kishi da riko da addini ba, to kamar tufka da warwara kenan.
Da wannan zan yi kira ga malamanmu cewar, gaskiya abinda ya shafi makarantun Islamiyyarmu sai an saka lura kuma an kawo masu dauki, don ganin an cinma tarbiyya irin ta Islama. Shawara ta ita ce; manyan malamanmu sai sun dawo sun rungumi makarantun nan, domin da za ka zagaya da dama daga ciki, sai k aga masu karantarwar mafiya yawansu matasa ne masu karancin shekaru, da karancin ilimi, alhali masu magana sun ce; (FAkIHUSHSHAI’I LA YU’UDIHI) wanda baida abu bai iya bada shi.
Matsalar itace, da farko da yaro ya iya kira’a sai ka ga ya zama malami. Ta biyu kuma za ka samu yana karantar da ‘yanmata wasu ma sun girme mashi. Ta uku kuma, sai ka samu yaro ko matashin da bai da aure amma yana karantar da matan aure. Wannan kira ne kuma don a gyara.
Abu na gaba d aya shafi makarantun boko, musamman masu zaman kansu, a gaskiya sai mun yi lura domin mafiya yawan su tarbiyya kawai suke bata wa.
Don haka ina kira ga al’umma da mu tashi tsaye, don ba wanda zai zo ya kawo mana gyara sai fa in mu muka nema da kawunanmu.
Makarantu tabbas nada tasiri, domin na san cewar a duk sati ko karshen wata ana tara yara a yi masu lacca wadda ta shafi rayuwar su da wajibci ko hakkokan da iyaye suke da shi akan su, a wani bangaren kuwa ‘yanmata a koya masu ilimin zaman aure da hakkokan miji da su kansu angunan in walimar biki ta tashi, malaman za su yi ruwa da tsaki ganin sun fadakar da su akan kula da hakkokan matan su. Kun ga anan, rashin samun ingantattun malamai ko shakka babu al’umma za ta tabarbare.
GWAMNATI (UWA MA BADA MAMA)
Wannana ginshiki shine na karshe, a nan gagarumar matsalar take saboda rashin saka hannun gwamnati akan abin da ya shafi tarbiyya da gyara akidu na mutane. Wannan kuma ya faru ne saboda irin tsarin mulkin da ake bi a kasar mu. Duk inda gwamnati ta Islama take, za ka ga akwai dokoki wadanda suka shafi sanya suturu ta kamala, sanya hijabi, wanda yanzu har yaran mu matasa maza suna sanya kayan arna irin su matsatsen wando kaji ana ambatar wane ya yi shiga ko aski irin na BALATOLI ko WIZZY, KO SWAGGA  da sauransu.
Haka gwamnati keda hakki na kula da kafafen yada labarai da kar su kuskura su saka wani shiri ko fim wanda ya saba wa addini ko al’ada. Kai, in zan ci gaba zan cinye duk filin akan nauyi da gwamnati take da shi wanda kuma shi ya ja  mana yanzu matasanmu ba su da kunya ba kuma tsoron Allah. Allah ya shiryar da mu baki daya.
Shawarwarin ku da gyara da karin bayani abune da zai taimaka mani matuka kasancewata mai karancin nazari da tunani dan haka sai ku tuntuban ta [email protected] ko 08065507271.
Sanusi Hashim Katsina,
Abban Sultana.