Iyaye mata da dama a jihar Kano sun gudanar da zanga-zanga ranar Laraba saboda batan ‘ya’yansu da ake zargin sace su aka yi tsawon shekaru.
Matan dake dauke da takardu da hotunan yaran da suka bata sun garzaya ofishin Hukumar Karbar Korafe-korafe da Hana Cin Hanci da Rashawa (PCACC) da kuma Hukumar Mata ta jihar don bayyana kokensu.
- Yadda Sarkin Kano ya kaiwa Kwankwaso ziyara kan rasuwar Mahaifinsa
- Kotu ta ba da umarnin yi wa matasa biyu bulala 12 a Kano
- Tsohon dan Majalisar Tarayya daga Kano ya rasu sanadiyyar COVID-19
Mai magana da yawun masu zanga-zangar, Zainab Abdullahi Giginyu, ta ce tsawon shekaru, gwamantin jihar ta nuna halin ko in kula game da damuwarsu.
A cewarta, tun daga shekara ta 2016, yara 118 ne aka sace kuma suke zargin an sayar da su ga wasu jihohin a Kudancin kasar nan.
Ta kara da cewa yawancin yaran da aka sace sun fito ne daga unguwannin Hotoro, Gama, Kawo da ‘Yankaba.
Ta ce sama da shekara daya kenan kwamitin na gwamnatin jihar Kano bai ce da su uffan ba game da lamarin batan yaran nasu.
Sai dai a nata bangaren, Kwamishiniyar Harkokin Mata ta jihar, Zahra’u Mohamed Umar da kuma shugaban PAACC, Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado, sun tabbatarwa da iyayen cewa za a bi musu kadinsu.
Aminiya ta rawaito, a baya sai da aka cafke wasu mutane da dama sannan aka gurfanar da su gaban kotu bisa zarginsatar yaran, ko da yake har yanzu an gaza sada yaran da iyayen nasu.