✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iyaye a rage nuna wa ’ya’ya so

A yanzu iyaye mata wadanda aka fi sani da kawaici da kunya a kan ’ya’yansu suna kokari su yaye lullubin kunyar da ya lullube idanunsu…

A yanzu iyaye mata wadanda aka fi sani da kawaici da kunya a kan ’ya’yansu suna kokari su yaye lullubin kunyar da ya lullube idanunsu ta yadda suke nuna son ’ya’yansu a fili.   A zahirin gaskiya babu mutumin da ba ya son dansa, amma wane irin so? Shin son da zai sa yaron ya zama shagwababbe ko kuma wanda zai sa ya zama ba ya shakkar kowa?

A da makwabci yana da cikakken iko da damar hukunta dan makwabcinsa idan ya ga ya aikata wani abin allah-wadai. Idan mahaifin yaron kuma ya zo ya ji labari babu abin da zai yi sai dai ya kara wa dan nasa wani sabon fadan ko kuma duka tare da yi wa makwabcin nasa godiya. Shin a yau haka abin yake?

A wannan zamani ta kai iyaye ba su so su ga wani ko da dan uwansu ne ya yi wa ’ya’yansu fada a kan wani abu da suke aikatawa na rashin daidai, ballantana kuma har ya kai hannunsa jikinsu. Idan suna jin kunya ne za su yi shiru sai dai shi mutumin ya gane kuskurensa ta wadansu hanyoyin, amma idan suka raina ajawalinsa to har gida cin mutunci zai iske shi.

Akwai  iyayen da saboda tsabar son ’ya’yansu babu wanda yake iya fitowa fili ya gaya musu laifukan ’ya’yan, sai su nuna rashin amincewarsu a kai, har ma su nuna cewa mutumin yana so ne kawai ya yi wa ’ya’yan baki. Idan ba a yi sa’a ba kuma daga wannan lokaci sun daura gaba da wannan mutumin ke nan.

Wannan shi ya kara iza wutar lalacewar tarbiyyar yaya a wannan lokaci, kiri-kiri mutanen unguwa suna kallon yara suna  aikata laifuka amma babu  wani wanda zai fito ya tsawata musu, ballantana kuma ya gaya wa iyayensu halin da ake ciki, ba don kaomi ba sai don tsoron abin da zai biyo baya.

A wadansu lokutan za ka ga uwa ta san danta yana aikata wani abu da bai dace ba, maimakon ta yi gaggawar sanar da mahaifinsa don daukar matakin da ya dace, musamman ma da yake yara sun fi jin tsoron iyaye maza fiye da mata, sai dai ta rika boye masa, wai don kada ya yi wa yaran fada. Ba tare da sanin cewa kanta take cuta ba, domin Hausawa sun ce itace tun yana danye ake tankwara shi. Sai ka ga wannan uba ba zai tashi sanin abin da dansa ke ciki ba sai abu ya gama lalacewa ya kai matakin da sai dai addu’a.

  Akwi matar da na sani kai ko da mijinta, wato mahaifin ’ya’yanta, ba shi da ikon ya yi musu fada a gabanta. Idan kuma har bacin rana ta sa ya yi hakan, to fa su sun samu lauya, domin ita za ta zama bakinsu ta kare su da dalilai irin nata. Kai wani lokacin ma sai ta gwaba wa mijin cewa wai shi wa ya san irin kuruciyar da ya yi? Ko kuma ta ce wai yara ne sai a hankali wata rana za su daina, da dai makamantan irin wadannan maganganu marasa tushe ballanatana makama. Idan kuma aka yi sa’a ba ta yi surutai ba, to fa mijin zai gane kurensa ta hanyar yin fushi da shi na tsawon lokaci.

Idan har ya kasance a matsayinki na uwa wacce ke ce a bangare marar karfi, domin kusan a ko’ina ’ya’ya sun fi raina uwa mace kasancewar ita ce a koyaushe ke tare da ’ya’ya, zai zama cewa kina nuna wa ’ya’yanki so a fili, ba ki son a fadi laifinsu, to kina cikin matsala babba. Ki sani ’ya’yan nan idan suka fahimci hakan za su iya aikata kowane irin abu a gabanki, sanin cewa babu abin da za ki iya aiwatarwa a kai.   

Ban da ma haka, duk dan da ya san cewa idan har ya yi laifi aka zo aka fada a gidansu iyayensa ba su daukar wani kwakkwaran mataki na yi masa fada, to fa ya samu lasisin da gobe ma zai je ya aikata wata aika-aikar da ta fi ta baya muni.

Akwai wani yaro da a yanzu ya yi nisa a fagen shaye-shayen miyagun kwayoyi, wanda kuma iyayensa ba su kai ga sani ba sai da abu ya lalace. Amma da aka zo ana tattauna maganar sai wadansu a unguwar suka bayyana cewa su sun dade da sani, amma sun ki fadi ne gudun kada iyayen yaron su dauki maganar a wata manufa ta daban.

A ganina tarbiyya  ba ta mutun daya ba ce, ma’ana ba a kan iyaye kadai take ba, abu ne da yake kan al’umma gaba daya, amma hakan ba zai yiwu ba sai da hadin kan iyaye. Kasancewar ba kowane lokaci ne iyaye ke tare da ’ya’yansu ba, ka ga akwai yiwuwar su iya aikata wadansu abubuwa ba a kan idanun iyayensu ba, ko kuma ma akwai yiwuwar su fita waje su aikata wani laifin da sun tabbatar ba za su iya aikatawa a gaban iyayensu ba, to ka ga a nan jama’ar gari za su iya taimaka muku wajen tsawata wa ’ya’yan.

Babu shakka a dabi’ar yaro yana son sakewa da walawa, ba ya son takurawa, don haka yana ganin duk wani wanda zai yi masa fada a matsayin mai takura masa. A matsayinki na uwa babu ruwanki da kallon fuskar da a lokacin da kike yi masa fada ko kuma kula cewa yana fushi ko kuma gudun kada dan ya dauke ki a matsayin wacce ba ta son sa da sauransu. Akwai lokacin da zai gane gaskiya ko ba dade ko ba jima.        

Idan har muna so lamarin tarbiyyar ’ya’yanmu ya tafi yadda muke so, to dole sai mun hada karfi da karfe mun ba sauran abokan zama fuskar da za su fito su gaya mana halin da ’ya’yanmu suke ciki ko kuma mu ba su damar hukunta ’ya’yan namu kai tsaye a duk lokacin da suka ga suna aikata ba daidai ba, musamman ganin irin yadda  yau ta zama yau.

Hausawa suna cewa, “ka ki naka duniya ta so shi. Haka kuma ka so shi duniya kuma ta ki shi.” Idan muka tsaya muka yi nazarin wannan magana za mu gane cewa akwai hikima babba a cikinta. Akwai kuma kalubale a gabanmu. Dole ne sai mun bude wa ’ya’yanmu idanu mun dora su a kan hanya ta gaskiya ko da ba sa so, sannan ne za su zama cikakkun mutane wadanda za su iya shiga cikin sauran jama’a su kuma yi mu’amala mai kyau.  Allah Ya sa mu dace, amin.