✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iyalai shida da mutum guda sun mutu sakamakon shan fate

Mutum bakwai sun mutu bayan sun sha fate-faten da aka sarrafa shi da gurbatacciyar albasa a Shiyyar Ajiya da ke garin Shinkafi a cikin Karamar…

Mutum bakwai sun mutu bayan sun sha fate-faten da aka sarrafa shi da gurbatacciyar albasa a Shiyyar Ajiya da ke garin Shinkafi a cikin Karamar Hukumar Shinkafi da ke jihar Zamfara.
Mukaddashin Gwamnan Jihar, Abdullahi Shinkafi shi ne ya tabbatar da hakan ga wakilin Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya a garin Gusau a jiya.
Shinkafi ya ce tuni gwamnati ta tura tawagar kwararrun likitoci zuwa yankin don gano musabbabin lamarin.
“Tuni suka dauki samfurin abincin, muna jiran su bamu sakamakon da suka samu don mu dauki mataki. Makusantan mamatan sun ce mutanen sun mutu ne sakamakon gubar da ke ganyen da aka yi faten da shi wanda a ka ce an hada shi ne da gurbatacciyar albasa. Ba za mu dogara da abin da muka ji ba muna jiran kwararraru su fito da sakamkon bincikensu”. Inji shi.
Mukaddashin gwamnan  ya ce shida daga cikin mamatan ’yan gida daya ne da suka hada da matar mai gidan da ’ya’yansa.
Ya ce mutum na bakwan makwabcin mamatan ne wanda shi ne ya ci abincin.
“Tuni na jagoranci tawaga ta musamman don jajantawa iyalan”. Inji shinkafi