Kasar Ivory Coast ta lashe Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka (AFCON) na 2023, bayan doke Najeriya da ci 2 da 1 a wasan karshe na gasar.
Mai masaukin bakin ta zama zakara ne, bayan ta warware kwallon da Najeriya ta jefa mata kafin tafiya hutun rabin lokaci.
- AFCON Final: Rigar Super Eagles ta yi ƙaranci a Kano
- Tura ta kai bango —Ma’aikatan Najeriya da ba a biya albashin Janairu ba
Dan wasan bayan Najeriya, Troost Ekoong ne ya fara jefa mata kwallo a minti na 38.
Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, Ivory Coast ta warware kwallon a minti na 62 daga hannun dan wasan tsakiyarta, Franck Kessie.
A minti na 81 Sebastian Haller ya kara wa mai masaukin baki kwallo ta biyu a raga, wanda hakan ya sanya ta zama zakarar AFCON ta 2023.
Idan ba a manta ba Najeriya ta doke Ivory Coast a wasan rukuni da suka fafata da ci daya ta hannun Troost Ekoong a bugun fanareti.