✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Italiya ta lashe Gasar Euro ta bana

Bayan an shafe minti 123, Italiya ta yi nasara a kan Ingila a bugun fanareti

Italiya ta doke Ingila a wasan karshe na Gasar Euro ta bans a bugun fenarati.

A wasan, dan wasan bayan Ingila Luke Shaw ne ya fara jefa kwallo a ragar Italiya a minti na biyu da fara wasa.

Bayan nan an yi ta fafatawa har zuwa minti na 67, lokacin da Leonardo Bonucci ya farke wa Italiya.

Haka aka ci gaba da gumurzu har na minti 123.

‘Yan wasan Italiya suna murna bayan da suka yi nasara a kan Ingila a Gasar Euro ta bana

A bugun fanaretin, dan wasan Italiya Domenico Berardi ne ya fara bugawa, sannan Harry Kane ya farke.

A bugu na biyu, dan wasan Italiya Andrea Belotti ne ya auna ragar, amma golan Ingila Jordan Pickford ya buge kwallon.

Barin fanareti

A bugu na uku Bonucci ya yi nasarar jefa kwallo a ragar Ingila, shi kuwa Marcus Rashford ya zubar.

A bugu na hudu ma, Federico Bernardeschi ya zura kwallo a ragar Ingila, shi kuma Jadon Sancho ya barar.

Dan wasan Ingila, Harry Kane, lokacin da yake wucewa ta gaban Kofin Euro kai a sunkuye bayan da ‘yan wasan Italiya suka nasara a kansu

Sai kuma bugun karshe, inda dan wasan Italiya, Jorge Luiz Frello Filho, wanda aka fi sani da Jorginho, ya bara, Bukayo Saka ma ya barar.

Idan ba a manta ba, a farkon fara Gasar Euro din, Bakin Raga ta yi hasashen cewa Italiya za iya lashe gasar.

A hasashenmu, Mubarak Abubakar ya ce Italiya ce za ta lashe gasar, shi kuma Salisu Musa Jegus ya ce Ingila ce za ta yi nasara.